Wata kotu da ke zamanta a Abuja ta bayyana kuskuren tsare tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya CBN, Godwin Emfiele ba tare da an gurfanar da shi gaban kotu ba.
Kotun ta ayyana tsarewar a matsayin kuskure da kuma take hakkin Emefiele.
- Gwamnati Ta Fara Binciken Ministar Jin ƙai Kan Umarnin Zuba Miliyan N585 A Asusun Ma’aikaciya – Minista
- EFCC Ba Samame Ta Kai Mana Ba – Dangote
Kotun ta yi Allah-wadai tare da cin tarar naira miliyan N100m ga gwamnatin tarayya da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC.
Ta kuma hana gwamnatin tarayyar da jami’anta sake kama Emefiele ko tsare shi ba tare da umarnin kotu ba.
Tsohon gwamnan na CBN ya roki kotu da ta umarci wadanda ake kara da su biya shi diyyar N1bn tare da hana su ci gaba da kama shi ko kuma a tsare shi.