Kotun koli ta tanadi ranar yanke hukunci kan karar da gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang ya shigar kan soke zabensa.
Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar da kotun daukaka kara duk sun bukaci gwamnan da ya sauka daga mukaminsa saboda zargin tafka kura-kurai wajen zaben fidda gwani wanda ya kai ga zaben gwamnan.
- ‘Yansanda Sun Kama Wani Matashi Da Buhunan Tabar Wiwi 45 A Katsina.
- Gwamnati Ta Fara Binciken Ministar Jin ƙai Kan Umarnin Zuba Miliyan N585 A Asusun Ma’aikaciya – Minista
Wani kwamitin mutane uku na kotun daukaka kara karkashin jagorancin mai shari’a Elphreda Williams-Dawodu ya bayyana Nentawe Goshwe na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Kotun daukaka kara ta kuma umurci hukumar zabe mai zaman kanta da ta janye takardar shaidar cin zabe da aka baiwa Mutfwang tare da ba Goswe sabuwar takardar shaidar lashe zabe.
Bayan sauraron lauyoyin dukkan bangarorin PDP da APC, kotun kolin ta tanadi ranar yanke hukuncin, inda ta ce, za ta sanar da bangarori biyun nan gaba kadan.