Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta sanar a jiya Laraba ranar 17 ga wata cewa, yawan GDP na kasar Sin ya karu da kashi 5.2 bisa dari a shekarar 2023 idan aka kwatanta da na shekara ta 2022. Yawancin rahotanni da sharhi na kafofin watsa labaru na kasa da kasa sun bayyana cewa, adadin ya yi daidai da yadda aka yi tsammani ko ma ya zarce.
Game da haka, a yau Alhamis ranar 18 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yayin taron manema labaru cewa, wannan ya nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin na farfadowa, da kuma samun ci gaba mai inganci. Ga duniya, wannan yana nufin akalla fa’idoji guda uku. Da farko shi ne kara azama ga tattalin arzikin duniya. Na biyu shi ne samar da kwanciyar hankali ga tattalin arzikin duniya. Na uku shi ne raba sabbin damammaki tare da sauran kasashen duniya.
Jami’ar ta jaddada cewa, muna da yakinin cewa, ci gaban tattalin arzikin kasar Sin mai inganci, da ci gaba da sa kaimi ga zamanintarwa irin ta kasar Sin, ko shakka babu za su kara samar da moriya ga duniya, da kara ba da gudummawa ga ci gaban duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)