Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Adon Da Kwalliya.
A yau kuma za mu kawo muku yadda uwargida za ta gyara gashinta a saukake.
Ga Abubuwan da za a tanada:
Man Shanu, Hular Gashi
Da farko za ki tsefe kanki ki taje shi, sai ki dakko man shanun ki rika tsaga gashin kina shafawa haka za ki yi kamar yadda ake shafa man kitso har ki gama kan gaba daya, sannan sai ki rika shasshafawa jikin gashin sai ki daure gashin, sannan ki dakko wannan hula ki sa ki barshi ya yi kamar awa daya zuwa biyu sai ki wanke za ki ga yadda gashinki zai zama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp