Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa daku a wannan makon a filin namu na Girki Adon Mata.
A yau shafin namu zai kawo muku yadda ake yin kayatacciyar miyar Agushi
A dai abubuwan da ake bukata
Agushi nikakke, Ganye Ugu, ki wanke, ki yanka. Alaiyaho ki gyara ki yanka, a wanke
Stock fish, Kwai, Tarugu, Albasa a jajjaga, Kifi, soyayyen nama, Magi, Kori, Gishiri,
Kayan kamshi, Manja da mangyada.
To ga kuma yadda ake hadawa
Da fari za ki dauko Agushinki ki diga masa ruwa kadan ki sa a turmi ki daka za ki ga yana hade jikansa har mai na fita daga jikinsa, idan kin gama sai ki dinga diban sa kina mulmula shi kamar karago haka za ki yi har sai kin gama.
Sai ki fasa kwanki ki sa albasa ki kada shi sosai ki ajiye a gefe shima, ki dauko kifinki ki cire kayan sai ki jika shi da ruwan zafi, sannan haka stock fish shima ki jika shi da ruwan zafi ko ki dora kan wuta ki tafasa har ya yi laushi.
Daga nan sai ki sanya tukunyarki akan wuta ki sa mangyada da manja ki yanka albasa ki soya sama-sama.
Ki dauko tarugu da albasarki ki sa a ciki ki soya sama-sama, sai ki kawo kayan kamshi, gishiri da maggi iya dandanon da zai yi miki. Ki dauko kwanki ki sa a ciki ki rufe tukunyarki ki rage wutar ki bar shi na dan wani lokaci sai ki bude ki juya shi ki sauke ki ajiye a gefe.