Kasar Sin da wasu kasashen Afirka da dama sun jaddada aniyarsu na tabbatar da ‘yancin kansu da kuma yin aiki tare don samun ci gaba tare, yayin da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya kammala ziyarar aiki ta kwanaki shida a nahiyar, wanda shi ne wuri na farko na ziyarar ministocin harkokin wajen kasar Sin a kowace sabuwar shekara cikin shekaru 34 da suka gabata.
A yayin ziyarar da ta kai ministan harkokin wajen kasar Sin Wang zuwa kasashen Masar, Tunisia, Togo da Cote d’Ivoire, shugabannin dukkanin kasashen hudu sun nuna goyon bayansu ga matsayin kasar Sin kan batun Taiwan, ta hanyar bayyana matsayinsu na kiyaye ka’idar Sin daya tak a duniya.
- Xi Jinping Ya Bada Muhimmin Umarni A Wajen Bikin Bayar Da Lambar Yabo Ta Injiniya Ta Kasa
- Mahalartan WEF: Sin Muhimmiyar Injin Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa
Da yake zantawa da manema labarai a jiya Juma’a, Wang ya ce, wannan wata cikakkiyar shaida ce ta al’adar Sin da Afirka na goyon bayan juna.
Ya kuma bayyana goyon bayan kasar Sin ga kasashen Afirka wajen kare ikonsu da ‘yancin kai, da nazarin hanyar zamanantarwa da ta dace da yanayin kasarsu. “Kasar Sin za ta ci gaba da kasancewa tare da Afirka.”
Wang ya kara da cewa, kasar Sin tana goyon bayan kasashen Afirka wajen hada kai da juna domin samun babban ci gaba, da kuma rike makomarsu a hannunsu.
Wang ya jaddada cewa, kamata ya yi kasashen Afirka su samu daidaiton ‘yanci a tsarin kasa da kasa, da damammaki a fannin ci gaban duniya, ya ci gaba da cewa, kasar Sin na tsayawa tsayin daka wajen tabbatar da daidaito a tsakanin dukkan kasashe ba tare da la’akari da girmansu ba, kana tana adawa da duk wani danniya da nuna fin karfi. (Yahaya)