Jiya Jumma’a ranar 19 ga wata bisa agogon wurin a birnin Fortaleza, shugaban kasar Brazil Luiz Inácio Lula da Silva ya gana da mamban ofishin siyasa na kwamitin koli na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi dake ziyara a kasar.
A yayin ganawar, shugaba Lula ya bayyana cewa, tun daga ranar farko da aka kulla huldar diflomasiyya, Brazil ta fito fili ta nuna goyon baya da kuma bin manufar kasar Sin daya tak, kuma za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan wannan matsayi a nan gaba. Shugaban ya kara da cewa, kasashen Brazil da Sin na da ra’ayin bai daya kan wasu manyan batutuwa da dama, kuma kasarsa na sa ran samun goyon baya daga wajen kasar Sin kan karbar bakuncin taron kolin G20 na Rio, da taron shugabannin kasashen BRICS, da babban taron sauyin yanayi na MDD, da dai sauransu, kana da yin aiki tare don kyautata harkokin dake shafar dukkan fadin duniya, da hada kai don karfafa karfin kasashe masu tasowa baki daya, da ma ikonsu na fada a ji a dandamalin kasa da kasa.
A nasa bangaren, mista Wang Yi ya nuna yabo kan yadda kasar Brazil take bin manufar Sin daya tak, da kuma goyon bayan da take nunawa ga halaltaccen matsayin kasar Sin, kana ya bayyana cikakken goyon bayan kasar Sin ga kasar Brazil wajen kara taka muhimmiyar rawa a harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, da samun nasarar karbar bakuncin tarurrukan bangarori da dama. (Mai fassara: Bilkisu Xin)