Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba zama sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminis ta Sin na birnin Fuzhou, fadar mulkin lardin Fujian dake gabashin kasar. A wancan lokacin, Fuzhou yana da tushe mai rauni na masana’antu da karancin kudaden shiga. Xi Jinping ya gudanar da bincike a birnin, daga bisani a watan Nuwanba na shekarar 1992, an zartas da shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma na shekaru 20 na birnin Fuzhou, inda aka bayyana cewa, za a dauki shekaru 3 wato zuwa shekarar 1995, wajen raya tattalin arzikin birnin inda zai ninka, idan aka kwantanta shi da shekarar 1990, za kuma a dauki tsawon shekaru 8 wato zuwa shekarar 2000, don sa kaimi ga raya birnin a dukkan fannoni zuwa matsayin birni na zamani a kasar Sin, kana za a shafe shekaru 20 wato zuwa shekarar 2010, inda bunkasuwar birnin za ta kai matsayin matsakaicin kasashe ko yankuna a nahiyar Asiya.
Xi Jinping ya maida hankali ga yankin teku a birnin. Fadin yankin teku na birnin Fuzhou ya kai muraba’in kilomita dubu 11, wanda ya yi daidai da na kasa a birnin. Don haka, an maida hankali ga raya yankunan gabar teku da yankunan teku dake birnin Fuzhou. Harkokin sufurin ruwa da masana’antu na gefen tashar jiragen ruwa suna bunƙasa, ilmin likitanci na fannin halittun teku, da samar da wutar lantarki ta karfin iska a kan teku da sauransu duk sun bunkasa. Kana an yi amfani da na’urorin zamani, da raya sha’anin kiwon kayan teku daga yankin teku kusa da kasa har zuwa yankin teku mai nisa. A shekarar 2022, yawan kudin da aka samu daga fannin teku a birnin Fuzhou ya zarce Yuan biliyan 330, wanda ya kai matsayin farko a kasar Sin a wannan fanni a shekaru da dama a jere.
Daga baya, an yi nasarar cimma burin ci gaban shekaru 8 na Fuzhou da kuma shekaru 20 kamar yadda aka tsara. Nasarorin da birnin Fuzhou ya samu suna da nasaba da shirin hangen nesa, da yin kokari har cimma buri. (Zainab Zhang)