Bisa gayyatar da shugaba Félix-Antoine Tshisekedi Tshilombo na Jamhuriyar Demokaradiyyar Kongo ya yi mata, wakiliyar musamman ta shugaban kasar Sin Xi Jinping, kana mataimakiyar shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama’ar kasar Sin Shen Yueyue, ta halarci bikin rantsar da shugaban kasar a Kinshasa, babban birnin jamhuriyar Demokradiyyar Kongo a ranar 20 ga watan Janairu. A jiya Lahadi ranar 21 ga wata kuma, shugaba Tshisekedi ya gana da madam Shen Yueyue a Kinshasa.
A yayin ganawarsu, madam Shen Yueyue ta isar da sakon gaisuwa da fatan alheri da shugaba Xi Jinping ya yi ga Tshisekedi. Tana mai cewa, kasar Sin na mai da hankali sosai kan raya dangantakar dake tsakanin Sin da Kongo Kinshasa, kuma a shirye take ta yi aiki tare da Kongo Kinshasa wajen aiwatar da muhimman ra’ayoyin bai daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, tare da nuna goyon baya ga juna kan muhimman muradunsu, da zurfafa hadin gwiwa irin na samun moriyar juna da cin nasara tare, da kuma ciyar da sada zumunta a tsakanin jama’ar kasashen biyu, kana da zurfafa yin mu’amala da hadin gwiwa bisa tsarin raya shawarar “Ziri daya da hanya daya” da na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, wato FOCAC, da nufin karfafa kyakkyawar dangantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen Sin da Kongo Kinshasa.
A nasa bangaren, Tshisekedi ya mika godiyarsa ga shugaba Xi Jinping bisa aiko da wakiliya ta musamman don halartar bikin rantsar da shi, ya kuma bukaci Shen Yueyue da ta mika sakon gaisuwa da fatan alheri ga shugaba Xi Jinping. Baya ga haka, Tshisekedi ya jinjina sosai ga ci gaban da aka samu a cikin shirin hadin gwiwa na RFI, wato amfani da ayyukan habaka albarkatu don inganta ayyukan samar da ababen more rayuwa a tsakanin Kongo Kinshasa da Sin. Haka zalika ya bayyana cewa, kasarsa tana mai da hankali sosai kan dadadden zumuncin dake tsakanin kasashen biyu, tana mai bin manufar Sin daya tak, da kuma fatan zurfafa hadin gwiwa da kasar Sin a wasu muhimman fannoni, ciki har da hakar ma’adinai da dai sauransu, don sa kaimi ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta kai wani sabon matsayi. (Mai fassara: Bilkisu Xin)