• English
  • Business News
Tuesday, October 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ya Kamata Kasashen Larabawa Su Dauki Darasi Daga Kasar Sin, Su Daina Biyewa Kasashen Yamma

by CMG Hausa
3 years ago
Larabawa

Rahoton Arab Barometer da kafar yada labarai ta BBC ta wallafa a baya bayan nan, ya ce kasashen Larabawa sun yanke kauna da tsarin demokuradiyyar kasashen yammacin duniya, saboda yadda tattalin arzikinsu ya yi rauni a karkashin tsarin.

Wannan rahoto ya tuna min da ziyarar da shugaban Amurka zai kai yankin gabas ta tsakiya a cikin wannan mako, wadda ya bayyana a matsayin mai muhimmanci ga tsaron kasarsa da kuma neman nasara a takararta da Sin.

  • Kasar Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dauki Jerinta Da Muhimmanci

Amurka ta gaza gane cewa, kan al’umma ya waye, babu wanda ke bukatar danniya da fifiko irin nata da kuma katsaladan da take yi cikin harkokin da ba su shafe ta ba. Kasashen sun ba ta dama, kuma sun ga aikin hannunta, sun ga yadda ta ingiza yake-yake ko ma kaddamar da yake-yake da tashin hankali a yankin.

Don haka, dukkan kasashe masu tasowa sun fahimci cewa, Amurka ita kanta kadai ta sani, ba ta damu da sauran kasashe ba.

A daya bangaren, a matsayinta na kasa mai tasowa, an ga yadda kasar Sin ke kiyaye cikakken ’yancin kasa da kasa da martabawa da mutunta su.

LABARAI MASU NASABA

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

An ga kuma irin jajircewarta wajen kyautata dangantakar moriyar juna da hadin gwiwar kasa da kasa. Kana ta zama misali na kasar da ta samu ci gaba na a zo a gani, bisa dabarun da ta dauka bisa la’akari da yanayinta, ba wai koyi da wata kasar yamma ba. Don haka, kasar Sin ta zama abun koyi a fannin tsarin demokradiyya da ci gaba.

Abun da ya kamata kasashen gabas ta tsakiyar su yi a yanzu shi ne, daukar darasi daga Sin, su tsara yanayin demokradiyyarsu ta hanyar da ta dace da muradu da moriyar al’ummominsu domin samun ci gaban da suke muradi.

Su kadai suke san yanayin da suke ciki da abun da ya fi dacewa da su, don haka su kadai ne za su iya magance matsalolinsu ba wai biyewa Amurka da kawayenta ba.

Ita kuma Amurka, kamata ya yi ta fahimci cewa, ba takara ya kamata ta yi da Sin ba, domin ba za ta ci nasara ba. Abun da ya kamata ta yi shi ne, hada hannu da kasar Sin a matsayinsu na manyan kasashe, domin samun moriyar juna da tallafawa tabbatar zaman lafiya a duniya da bunkasa tattalin arzikinta da gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya a duniya. (Fa’iza Muhammad Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka
Daga Birnin Sin

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

October 20, 2025
Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar
Daga Birnin Sin

Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

October 20, 2025
Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

October 20, 2025
Next Post
Kalubalen Rashin Tsaro: Ba Za Mu Kara Cewa Buhari Uffan Ba – ACF

Kalubalen Rashin Tsaro: Ba Za Mu Kara Cewa Buhari Uffan Ba – ACF

LABARAI MASU NASABA

Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa

Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa

October 21, 2025
Mutane 3,433 Sun Rasu a Hatsarin Mota 6,858 Cikin Wata 9 A Nijeriya – FRSC

Mutane 3,433 Sun Rasu a Hatsarin Mota 6,858 Cikin Wata 9 A Nijeriya – FRSC

October 21, 2025
NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Don Biyan Buƙatun ASUU Da Sauran Ƙungiyoyi 

NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Don Biyan Buƙatun ASUU Da Sauran Ƙungiyoyi 

October 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

’Yansanda Sun Kama Ɗan Fashi Sanye Da Kayan NYSC A Enugu

October 21, 2025
Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

October 21, 2025
Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

October 20, 2025
An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

October 20, 2025
Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

October 20, 2025
Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

October 20, 2025
Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

October 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.