Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yana sane da matsalolin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta dangane da tsadar rayuwa da rashin tsaro.
Ya bayyana haka ne a mahaifarsa ta jihar Katsina a lokacin da yake gabatar da sakonsa ga ‘yan Nijeriya na bukukuwan Sallar Eid-el-Kabir.
A wata sanarwa da Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ya fitar, Buhari ya ce ana ci gaba da kokarin lalubo hanyoyin magance wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke fuskanta, ya kara da cewa gwamnatinsa kuma na ci gaba da jajircewa wajen inganta tsaron kasar.
“Ba zan huta ba har sai na kawo dauki ga ‘yan Nijeriya. Ina sane da matsalolin da mutane ke fuskanta kuma ina aiki tukuru don magance su, “in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp