Tsohon jami’in gwamnatin Australia Micheal Keating, ya ce Amurka na dagewa wajen daukar kasar Sin a matsayin barazanar tattalin arziki, amma ta gaza fahimtar yadda ci gaban tattalin arzkin kasar ta nahiyar Asiya ke amfanawa duniya.
Ya ce duk da tana fuskantar matsaloli a cikin gida kamar na tsayawar biyan kudin kwadago da karuwar rashin daidaito, Amurka ta ki amincewa cewa koma bayan da take fuskanta, laifinta ne.
- Bankunan Kasashen Ketare Sun Yaba Da Bunkasuwar Tattalin Arzikin Kasar Sin
- Auren Gata : Gwamnatin Jihar Kebbi Ta Aurar Da Mata 300
Maimakon haka, sai take neman wanda za ta dorawa laifi, inda ta dauki ci gaban tattalin arzikin kasar Sin a matsayin wata dama mai sauki ta dora laifin.
Micheal Keating, wanda tsohon jami’in gwamnatin Australia mai ritaya ne ya kuma yi watsi da abun da ake kira da wai “barazanar mota” ta kasar Sin. Ya kuma zayyano wasu kyawawan dalilai na yin maraba da motocin kasar Sin maimakon daukarsu a matsayin barazana, kamar masu amfani da lantarki, domin farashinsu mai sauki da kuma hanyar rage hayakin Carbon.
Ya kara da cewa, akwai yuwuwar Australia za ta ci gajiyar kasuwar motoci ta kasar Sin. (Fa’iza Msutapha)