Masu masaukin baki sun fitar da kasar Senegal daga kofin gasar kwallon kafa ta kasashen Afirika, AFCON 2023 da ake ci gaba da gudanarwa a kasar ta Cote de’Voire.
Habib Diallo ne ya fara jefawa kasar Senegal kwallo a minti na 4 da fara wasa kafin Frank Kessie ya farkewa masu masaukin bakin kwallo a wani bugun daga kai sai mai tsaron raga da ya samu a minti na 86.
- AFCON 2023: Guinea Ta Doke Equatorial Guinea A Wasan Zagaye Na 16
- Kotun Ƙoli Ta Jingine Hukuncin Zaɓen Gwamnan Adamawa
Hakan yasa alkalin wasa Piere Atcho ya kara mintuna 30 domin cigaba da fafatawa, bayan kammala mintuna 30 na karin da akayi ba tareda wani ya jefa kwallo ba.
Sai aka tafi zuwa bugun daga kai sai mai tsaron raga inda kasar Senegal ta jefa kwallaye 4 a raga, yayin da Ivory Coast ta jefa duka kwallaye biyar da ta buga.