Fitaccen mawaki kuma dan fafutukar kare hakkin dan Adam, Seun Anikulapo-Kuti, ya zargi jami’an rundunar ‘yansandan Nijeriya da alhakin aikata manyan laifukan garkuwa da mutane a Nijeriya.
Da yake magana game da karuwar sace-sacen da aka yi a baya-bayan nan a cikin wani faifan bidiyo da bai dade ba wanda ya fito a ranar Talata, Seun ya bayyana jami’an ‘yansandan Nijeriya a matsayin “babbar kungiyar masu garkuwa da mutane” a kasar.
Ya ce, yana da hujjar fadar hakan ne akan abinda ya samu daga ofishin jami’an yayin da ake tsare da shi a ofishin ‘yansanda da ke Panti, Legas, a shekarar da ta gabata saboda ya ci zarafin wani dan sanda.
Cikakkun bayanai na zuwa daga baya…