Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika sakon taya murna ga takwaransa na kasar Nauru David Ranibok Adeang yau Laraba, inda ya taya Nauru murnar cika shekaru 56 da samun ’yancin kai.
Xi ya bayyana cewa, kwanan nan Sin da Nauru suka maido da huldar diplomasiya tsakaninsu a hukumance, matakin da ya bude sabon babi na dangantakar bangarorin biyu. Shugaba Adeang ya yanke shawarar siyasa ta amincewa da manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, tare da yaba wannan manufa.
Xi ya kara da cewa, yana dora muhimmanci sosai kan ci gaban bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Nauru. Yana kuma fatan yin aiki tare da shugaba Adeang wajen zurfafa amincin siyasa a tsakaninsu, da inganta hadin gwiwa mai inganci, da karfafa mu’ammalar al’adu tsakanin bangarorin biyu, ta yadda hakan zai kawo alheri ga al’ummun kasashen biyu. (Safiyah Ma)