Tsohon shugaban kasar Habasha, Mulatu Teshome ya bayyana cewa, an yaba da shawarar da kasar Sin ta gabatar, game da batun zaman lafiya da ci gaba a yankin kahon Afirka (HOA) a wani mataki na tallafawa kasashen yankin tinkarar kalubalen tsaro, da ci gaba da shugabanci, dake addabar su.
Daga ranar 20 zuwa 21 ga watan Yunin da ya gabata ne, aka gudanar da taron zaman lafiya da shugabanci na gari da raya kasa tsakanin Sin da yankin kahon Afirka karo na farko a birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha.
Babban taron zaman lafiya da ci gaban yankin, ya hallara ministoci da manyan jami’an gwamnatin kasashen yankin kahon Afirka, da suka hada da Habasha, da Kenya, da Sudan, da Sudan ta Kudu, da Somaliya, da Uganda da kuma Djibouti, da kuma Xue Bing, wakilin musamman na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin mai kula da harkokin yankin kahon Afirka.
Tsohon shugaban kasar ta Habasha ya jaddada cewa, zaman lafiya da kwanciyar hankali na da muhimmanci ga ci gaban kowace kasa, inda ya ba da misali da kwarewar kasar Sin wajen samun bunkasuwa cikin lumana.
Ya bayyana cewa, labarin nasarorin da kasar Sin ta samu, da ci bunkasar tattalin arzikin kasar, sun samu ne sakamakon yadda kasar take zaune lafiya har ma da makwabtanta.
Don haka, ya ce muna bukatar al’umma mai zaman lafiya da kwanciyar hankali, kuma idan babu zaman lafiya da kwanciyar hankali, babu wanda zai zo ya zuba mana jari.”
Ya kara da cewa, kasashen yankin kahon Afirka sun gamsu cewa, muna bukatar zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, kuma kokarin da kasar Sin ke yi na saukakawa da kuma hada kan kasashen dake makwabtaka da juna, don tattauna batun zaman lafiya da tsaro da ci gaba na da matukar muhimmanci.
Ya ce, yana fatan kasar Sin za ta ci gaba da karfafa wa yankin gwiwa, wajen tattauna batun zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Kuma idan Habasha da makwabtanta suna zaman lafiya, hakika za mu ci gajiyar hakan.” (Ibrahim Yaya)