A ranar 3 ga wata bisa agogon wurin, an gudanar da taron masu wasanni na wucin gadi wato Flash mob, game da shagalin murnar bikin bazara na gargajiyar kasar Sin mai taken “Gabatarwar murnar bikin bazarar gargajiya ta kasar Sin da kallon shagalin bikin bazara na CMG” a tashar Labu ta layin dogo na Addis Ababa zuwa Djibouti dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.
A dandalin Meskel da ke tsakiyar birnin Addis Ababa, an kuma nuna faifan bidiyo na tallata shagalin murnar bikin bazara na kasar Sin na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice, wanda ya kawo yanayin murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin a Habasha dake gabashin Afirka.
- Li Qiang Ya Tattauna Da Kwararrun ‘Yan Kasashen Waje Dake Kasar Sin
- Cibiyar Harbar Kumbuna Ta Xichang Ta Kasar Sin Ta Cimma Nasarar Aiwatar Da Harbi Zuwa Sararin Samaniya Karo Na 200
Bugu da kari, daga ran 2 ga wata, an nuna shirin bidiyo da CMG ya tsara don dandanon liyafar murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin a rukunin gidajen sinima na AMC da sauransu, inda za a nuna wannan bidiyo sau fiye da dubu 60 a allunan talabijin 1169.
An watsa wannan shirin bidiyon a manyan birane 8 na Amurka, kafin a fara gabatar da fina-finan, a sa’i daya kuma, an gabatar da shi a zagaye a wurin hutu da sayar da tikiti a cinima.
An ce, an kafa rukunin AMC a shekarar 1920, ya kasance rukuni mafi girma a duniya, dake rike da yawancin kasuwannin cinima a Amurka. Ban da wasu manyan birane da a baya ake gabatar da irin wannan bidiyo a shekarar 2023, a wannan karo kuma, AMC ta kara gabatar da irin wannan bidiyo a biranen Boston, Houston, Dallas da dai sauran birane, abin da ya alamanta cewa, liyafar bikin bazara ta CMG ta kara habaka tasirinta ga masu kallo na Amurka.
A waje daya kuma, a ran 2 ga wata, an nuna wannan shirin bidiyo a wata gasar wasan kwallon gora ta Rasha da aka gudanar a filin wasa na Mytishchi dake arewa maso gabashin kasar Rasha, shirin bidiyon ya jawo hankalin ‘yan kallo matuka tare da samun karbuwa.
Wasu ’yan kallo sun bayyana cewa, wannan ne karon farko da suka kalli bidiyon dandanon bikin CMG a gasar wasan kwallon gora na kankara, kuma sun nuna sha’awa tare da gamsuwa matuka. Har ila yau, sun aike da gaisuwar sabuwar shekara ga jama’ar kasar Sin, tare da fatan hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Rasha da Sin da al’ummomin kasashen biyu za su karfafa, kuma zumuncin ya dore har abada. (Bilkisu Xin, Amina Xu)