Sanata mai wakiltar Adamawa ta Arewa, Elisha Abbo, ya bayyana dalilan da ya sa ya bar kungiyar yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.
Bayan fitowar sanarwar cewa, tsohon Gwamna Borno, Kashim Shettima shine mataimaki ga Tinubu, ba jimawa Abbo ya bayyana ficewarsa daga kungiyar goyon bayan Tinubu.
A cewarsa, amincewar tikitin tsayawa takarar musulmi da musulmi da jam’iyyar APC ta yi, a na shi ra’ayin bai dace ya ta ta ‘yan takarar yakin neman zaben shugaban kasa a jam’iyyar APC ba.
Ya kuma bayyana zabin jam’iyya mai mulki na tikitin musulmi da musulmi a matsayin “rashin tunani da rashin sanin tsarin siyasar Nijeriya.”
A yayin da yake zantawa da tashar talabijin ta Arise TV kan rashin jin dadinsa da matakin da kuma ficewarsa daga kungiyar yakin neman zaben, Abbo ya ce duk da cewa ya goyi bayan Tinubu a baya, ba zai iya ci gaba da biyayya ga gwamnatin da ta karya kundin tsarin mulkinta ba.