Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, na jihar Adamawa, ya tabbatar wa al’ummar jihar kudurin da ya rataya a wuyan gwamnatinsa na ganin ta gurfanar da mutanen da suka hadabaki, da dakatacce kwamishinan hukumar zabe ta kasa (INEC) a jihar, Hudu Yunusa Ari, kan rawar da ya daka a babban zaben 2023.
Ahmadu Umaru Fintiri, ya bayyana haka lokacin da yake yiwa jama’ar jihar jawabi da aka watsa kai tsaye ta kafofin sadarwa ranar Litinin, ya ce “mu na iya mu kare tsarin zabenmu da dimokuradiyya daga cin zarafin da bai kamata ba.
- Zaɓen Cike-gurbi: PDP Ta Lashe Zaɓen Ɗan Majalisar Jiha A Mazaɓar Mayo-Belwa A Adamawa
- Hukuncin Zaben Adamawa: Na Rungumi Kaddara – Binani
“It’s kanta kotun Koli a cikin hukuncinta ta yi Allahwadai da matakin da Hudu Ari ya dauka, ta ce matsayin wani aiki ne na ‘rashin hankali da aikata laifuka’ wanda ya jefa harkar dimokradiyya cikin kunya.da dimauta” inji gwamnan.
Haka kuma gwamna Fintiri, ya nuna gamsuwa da yadda alkalai a matakai daban-daban na kotuna suka jajirce wajen warware rudun da’aka kawo a matakai daban-daban tare da fitar da hukuncin da ya dace da al’ummar jihar Adamawa.
Ya ce “hukuncin da kotun koli na ranar 31/01/2024, ya kawo karshen duk wata hayaniyar zaben 2023 a Adamawa, kwanakin karya da yaudara sun kare, lokacin farfagandar karya da maganganun son zuciya sun shude.
“Dole na yabawa hukumar zabe INEC da ta tsaya tsayin daka ta kare mutumci da kimarta ta gujewa son zuciya, lokacin da Kwamishina Hudu Ari, ya aikata son zuciya da rashin bin ka’idar doka” inji Fintiri.
Gwamna Ahmadu Fintiri, ya ce duk da yanzu ba lokacin takara ba ne, amma jihar Adamawa jiha ce ta jam’iyyar PDP, kamar yadda aka gani lokacin zabuka da kuma a yadda ta kasance a kotuna, anga yadda mutanen suka yi magana da katunan zabe.
“Shaidar hakan ita ce sabuwar nasarar da PDP ta samu a zaben dan majalisar dokokin jiha mai wakiltar mazabar karamar hukumar Mayo-Belwa, mu na kara godiya ga masu kada kuri’a da suka kara sanya nasara a kan hukuncin da kotun koli ta yanke” ya jaddada.
Gwamna Ahmadu Fintiri, ya kuma baiwa jama’ar jihar tabbacin gwamnatinsa za ta ci gaba da musu hidima, tsare-tsare da kyautata rayuwa, ilimi kyauta, samar da kiwon lafiya, kayayyakin more rayuwa a birane da karkara, karfafa mata da matasa da sauransu.