Da yammacin gobe Juma’a 9 ga wata da dare, agogon Beijing, za a watsa shagalin murnar Bikin Bazara da babban rukunin gidajen talabijin da rediyo na kasar Sin CMG ya shirya, ga masu kallo a fadin duniya, kamar yadda aka tsara.
Sassan gidan talabijin na CGTN na kasar Sin masu amfani da harsuna 68, za su hada gwiwa da kafofin yada labarai sama da 2100 daga kasashe da yankuna 200 dake fadin duniya, ciki har da na Amurka da Canada da Birtaniya da Faransa da Jamus da Afrika ta Kudu da Kenya, domin watsawa tare da bayar da rahotannin shagalin bikin.
Shagalin wanda kundin bajinta na Guinness ya ayyana a matsayin shirin talabijin da ya fi samun masu kallo a duniya, ya zama wata al’ada ga Sinawa a fadin duniya na murnar shiga sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin, haka kuma ya samar da wata kafa ga duniya ta fahimtar al’adun Sinawa da sabuwar shekarar gargajiyarsu. (Fa’iza Mustapha)