A Cikin wata sanarwar jami’in yada labaran gidan gwmnatin Adamawa, Wonosikou, ya sanyawa hannu, ta ce Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, ya haramta jigilar kayayyakin gine-gine ta kan iyakokin kasar zuwa kasashe makwabta.
Sanarwar ta ce, matakin da gwamnan ya dauka zai taimaka wajen takaita hauhawar farashin kayayyakin gini, ya umurci dukkanin hukumomin tsaro da ke aiki a yankunan kan iyakokin jihar da kasashe makwanta da su kara sa ido tare da hana manyan motocin jigilar kayayyaki zuwa kasashen waje.
- Jam’iyyun Hamayya Ku Zo Mu Haɗa Kai, Mu Gina Jihar Adamawa – Fintiri
- Ku Je Ku Magance Matsalar Yunwa Da Ta Addabi Jama’a -Fintiri
Gwamna Fintiri ya yi gargadin cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen kame motocin da ke jigilar irin wadannan kayayyaki ta kan iyaka tare da gurfanar da duk wanda aka kama gaban kuliya.
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya nuna damuwarsa kan wasu ayyukan ‘yan Nijeriya marasa kishin kasa ya marasa, ya yi kira da jama’a da su taimaka wa jami’an tsaro wajen yakar wannan barazanar ta hauhawan farashin kayayyakin gini.