A kwanan baya ne kasar Sin ta sanar da shirinta na samar da karin makamashin da ake iya sabuntawa, inda bayanai ke nuna cewa, karin wutar lantarkin da kasar ta samar ta makamashin da ake iya sabuntawa, zai wuce kaso 50 cikin dari bisa na wutar lantarkin da al’ummar kasar za ta yi amfani da shi, ya zuwa shekarar 2025.
A shekarun baya, kasar Sin ta samu karin ci gaba a bangaren sarrafa makamashin da ake iya sabuntawa, inda yawan injunan samar da makamashin da take samu yana kan gaba a duniya, kana kasar ta samu kwarewa a fannin fasahohin sarrafa makamashin da ake iya sabuntawa, da aikin raya masana’antu na wannan bangare.
Bisa shirin da aka tsara, zuwa shekarar 2025, yawan wutar lantarkin da kasar za ta samar ta makamashin da ake iya sabuntawa, zai kai kimanin KWH triliyan 3.3 a duk shekara. Game da haka, mista Li Chuangjun, babban darektan sashen sabbin makamashi na hukumar makamashin kasar Sin, ya ce,
“A shekarar 2020, kasarmu ta samar da wutar lantarkin da yawansa ya kai KWH biliyan 2.2 ta makamashin da ake iya sabuntawa. Daga wannan adadi zuwa biliyan 3.3, za a samu karuwar da ta kai kashi 50%.”
Ban da wannan kuma, shirin da kasar Sin ta gabatar ya nuna cewa, kasar za ta ci gaba da kokarin hadin gwiwa tare da sauran kasashe, ta fuskar sarrafa sabbin makamashi masu tsabta, da inganta fasahohi da masana’antu masu alaka da wannan bangare. (Bello Wang)