Gwamnatin jihar Zamfara ta fara biyan bashin naira biliyan 13.4 na kudaden tallafi ga wadanda suka yi ritaya a jihar.
Gwamnatin jihar ta kafa kwamiti don ya fara tantance bayanan ma’aikatan da suka yi ritaya don biyan basussukan garatuti daga shekarar 2011 zuwa yau.
- Gwamnan Zamfara Ya Kaddamar Da Kwamitin Asusun Samar Da Tallafin Tsaro
- Matsalar Tsaro: Gwamna Dauda Ya Kaddamar Da ‘Askarawan’ Zamfara
Kakakin yada labaran Gwamnan Jihar, Sulaiman Bala Idris, ne ya bayyana haka a wata takarda da aka raba wa manema labarai a jihar.
A cewar takardar, wadanda suka yi ritaya da suke bin bashin garatuti tun daga shekara ta 2011 tuni suka fara karbar kudadensu.
“Gwamnatin jihar ta dauki wani muhimmin matakai na biyan basussukan da tsofaffin ma’aikatan da suka yi ritaya ke bi, da wadanda suka mutu. Cewarsa.