Ɗan Majalisar tarayya mai wakiltar Katsina ta tsakiya Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya ɗauki nauyin biyan kuɗin karatun ɗalibai ‘yan asalin Ƙaramar Hukumar Katsina su 60.
Ɗaliban za su yi karatu ne a reshen jami’ar Ahmadu Bello da ke da mazauni a kwalejin ‘ Gial College of Higher Education, Katsina ‘ domin yin karatu a ɓangarori da dama.
Da yake ƙaddamar da ba da tallafi ɗan majalisar wanda ya samu wakilcin mai taimaka masa na musamman Hon. Abdulrazaq Yahaya ya ce wannan wani ɓangare ne na alƙawarin da ya ɗauka a lokacin yakin neman zaɓensa.
A cewar sa, ɗalibai 60 ne za su amfana da wannan tallafi, kuma an zaɓo su ne daga cikin ƙaramar hukumar Katsina ta tsakiya.
‘Wadannan Ɗalibai za su yi karatun difolama ne a kwalejin ‘Gial College of Higher Education ‘ a ɓangarori guda shida da suka haɗa da bangaren turanci da ilimin lissafi da ilimin kimiyyar ɗakin karatu da kuma ɓangaren Hausa’ in ji A.Y
A cewar sa, sauran kwasa-kwasan sun haɗa da da bangaren Addinin Musulunci da kuma ilimin kimiyya da zumar cewa su ne kashi na farko kuma ana sa ran cewa nan gaba kaɗan wasu ma za su amfana a sauran ɓangarori
Ho. Abdulrazaq Yahaya ya ja kunnen ɗaliban da su maida hankali a wajen wannan karatu na su domin su zama madubi ga sauran al’umma tare da fita kunyar wanda ya ɗauki nauyin karatun nasu.