Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Adams Oshiomhole, ya soki manufofin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda yake ganin cewa, sune musabbabin halin da ‘yan Nijeriya ke ciki.
Oshiomole ya nesanta kansa da manufofin tsohon shugaban kasar, sannan ya kuma nuna yadda suka dagula tattalin arzikin kasar nan da kuma illar da suka haifar.
- Ɗan Majalisa Ya Ɗauki Nauyin Kudin Makarantar Ɗalibai 60 A Katsina
- Shugabannin Kasashe Da Hukumomin Duniya Sun Taya Sinawa Murnar Shiga Sabuwar Shekarar Gargajiya
Oshiomhole, ya wanke shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kuma zargin da ‘yan kasa ke masa na ganin shi ne sanadin halin da ake ciki, inda ya ce, Shugaban ya karbi kasar ne a haka kuma yana kokari wajen ganin ya saitata.
A wani labarin makamancin hakan, tsohon Gwamnan CBN, Sanusi Lamido Sanusi, inda ya yabawa manufofin Tinubu kuma ya danganta kalubalen tattalin arzikin da rashin gudanar da iya Mulki da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi.