Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta bayyana cewar kocin kungiyar Roy Hodgson ka iya rasa aikinsa a matsayin mai horar da kungiyar matukar al’amura suka cigaba da tafiya a haka.
Hodgson wanda ya maye gurbin Viera a farkon kakar wasa ta bana ya yi rashin nasara a wasan da kungiyar ta buga da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a karshen makon da ya gabata.
Zuwa yanzu dai Palace tana matsayi na 15 a teburin Firimiya,yayinda ake alakanta tsohon kocin Einchtract Frankfurt Oliver Gasner da maye gurbin Hodgson mai shekaru 76.