Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya amince da kafa wani kwamiti mai mambobi 27 da zai tabbatar da dokar sa ido kan masu boye hatsi da kuma masu tsanananta kudin haya a jihar.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar, Adullahi Aliyu-Yar’adua, ya fitar a Katsina ranar Lahadi.
- Wadanne Irin Abinci Ya Kamata Ku Kiyaye A Lokacin Al’ada?
- Liu Jianchao Ya Halarci Babban Taron Kafa Dandalin Tattaunawa Na Jam’iyyun Siyasar Kasa Da Kasa
Idan dai ba a manta ba, a kwanakin baya ne gwamnatin jihar Katsina ta haramta boye kayan abinci da sauran kayayyakin masarufi a jihar.
A cewarsa, gwamnatin ta ba da umarnin tabbatar da bin ka’idojin inganta samar da abinci a jihar da kuma gano mutanen da ke boye kayan abinci.
Aliyu-Yar’Adua ya ce, kwamitin zai kuma cafko masu ruwa da tsaki wajen haifar da tsadar kayayyaki da kuma gurfanar da su a gaban kotu.
Ya ce, kwamitin zai kasance karkashin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, Alhaji Jabiru Tsauri yayin da Kwamishinan shari’a, Fadila Dikko; kwamishinan yada labarai da al’adu, Dr Bala Zango, da kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida. Dr Nasiru Danmusa za su zama mambobin kwamitin.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da wakilan rundunar sojin Nijeriya, ‘yansandan Nijeriya, kungiyoyin sa kai, shugabannin al’umma da na addini, kungiyar dillalan hatsi da dai sauransu.
Ya ce, ana sa ran gwamnan zai kaddamar da kwamitin a ranar 21 ga watan Fabrairu.