Haramtacciyar kungiyar da ke rajin kafa yankin Biafra (IPOB) ta gargadi babbar kwamishiniyar Birtaniya a Nijeriya Catriona Laing da ta gaggauta soke shirinta na kai ziyara shiyyar Kudu Maso Gabashin kasar nan ko kuma ta dandana kudarta.
IPOB ta yi gargadin ne a wata sanarwar da ta fitar inda ta yi barazanar cewa za a kashe Wakiliyar muddin ta yi wannan ziyarar.
IPOB, ta ce bisa bayanan sirri da suka samu akwai shirin kashe jakadar Birtaniya din daga bisani a daura laifin hakan ga mambobinsu.
Don haka ne ma suka ce maganin bari ma kar a fara don haka kar ta ma kai ziyarar kawai domin kiyaye rayuwarta.
A sanarwar daraktan yada labarai IPOB, Emma Powerful ya fitar a ranar Alhamis gami da raba wa ‘yan jarida, sun ce, “Indigenous People of Biafra karkashin jagorancin shugabanmu Mazi Nnamdi Okwuchukwu Kanu, muna son shawartar babbar kwamishiniyar Birtaniya Catriona Laing da ta shiga taitayinta ta san wuraren da za ta ke jefa kafarta a ciki.
“Sannan muna kira a gareta da ta yi taka-tsantsan da yawo a sassan Nijeriya musamman yankunan Biafra kai tsaye ma shiyyar Kudu Maso Gabas.
“Dalilan wannan kiran shine don kiyaye lafiyarta da rayuwarta da kokarin ceton rayuwarta. Muna mutanta rayuka musamman na masu kawo ziyara yankunanmu.”