Gabanin sake zaben cike gurbi na majalisar dokokin jihar a mazabar Kunchi/Tsanyawa da aka shirya gudanarwa a watan Maris na wannan shekara, rundunar ‘yansandan jihar Kano ta gargadi manyan jam’iyyun siyasa kan tayar da tarzoma ko kuma tada zaune tsaye a jihar.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Muhammad Usain Gumel ne ya yi wannan gargadin, inda ya gargadi shugabannin jam’iyyu da magoya bayansu kan ayyukan ‘yan daba da magudin zabe.
- NAF Ta Kama Shahararren Mai Garkuwa Da Mutane A Karamar Hukumar Takai A Jihar Kano
- Zargin Baɗala: Kotu Ta Umarci A Binciki Lafiyar Ƙwaƙwalwar Murja Kunya
Manyan jam’iyyun siyasa biyu da za su fafata a zabukan da za a sake karawa, su ne APC da NNPP, sun kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tare da yin alkawarin bin ka’idoji a lokacin zabe da kuma bayan zabe.
Gumel ya yi wannan gargadin ne a wata ganawa da ya yi da shugabannin jam’iyyun siyasa, kungiyoyi masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki a taron da rundunar ‘yansanda a jihar ta shirya a jiya Talata, a wani mataki na tabbatar da gudanar da zabukan ba tare da tangarda ba.