A lokacin bikin bazara na shekarar da muke ciki, na tafi birnin Sanya na lardin Hainan, tsiribin dake kudancin kasar Sin, wurin da ya shahara matuka a duniya ta fuskar yawon bude ido. Jirgin saman da na shiga ya cika makil da mutane, ban da wannan kuma jiragen ruwa da kasuwannin wurin sun yi cunkoso matuka, abun da ya nuna wani yanayi mai kyau a bangaren sayayya na kasar Sin.
Bisa alkaluman da ma’aikatar al’adu da yawon shakatawa ta Sin ta gabatar, a yayin hutun bikin bazara na kwanaki 8, yawan mutanen da suka yi yawon bude ido a nan kasar Sin ya kai miliyan 474, kana yawan kudin da aka kashe a kasuwannin kasar ya kai kudin Sin RMB Yuan biliyan 630 kwatankwacin dalar Amurka kimanin biliyan 87.7, adadin da ya samu karuwa matuka bisa na makamancin lokaci na shekarar 2023.
- Sin Ta Sha Alwashin Kare ‘Yancin Kamfanoninta Bisa Doka
- Jirgin C919 Na Sin Ya Halarci Bitar Bikin Nune-nune Jiragen Sama Na Singapore
Ta wadannan alkaluma ake iya ganin yanayin farfadowar tattalin arzikin Sin. Sa’an nan, farfadowar tattalin arzikin Sin kuma ya karawa mutanen kasashe daban daban kwarin gwiwa game da ci gaban tattalin arzikin duniya. Bisa alkaluman da aka bayar, yawan Sinawa da suka yi yawon bude ido a ketare a wannan lokaci, ya kai kimanin miliyan 3.6, abin da ya ingiza sana’ar yawon bude ido da otel da kuma samar da abinci a wuraren da Sinawa suka je.
Karuwar yawan sayayya a sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, ta bayyana boyayyen karfin kasuwar sayayya na Sin da yanayi mai armashi na bunkasuwar tattalin arzikin Sin, wanda ya zama karfin jagora mai kyau ga ci gaban tattalin arzikin kasar a sabuwar shekarar da muke ciki. Ban da wannan kuma, ya baiwa mutanen mabambantan kasashe cikakken kwarin gwiwa game da samun farfadowar tattalin arzikin duinya yadda ake bukata. (Mai zana da rubutu: MINA)