ADAMU ISA HUSA wani masihin matashi ne wanda Allah ya yi masa baiwar kere-kere da kuma hada kayayyakin injinoni da na’urori daban-daban wanda ya ke yi da kansa. Matashin mai shekaru da ba haura 40 ba, ya bayyana yanda wannan baiwar ta faro, da kuma yanda aka yi. A cikin hirar musamman da shafin kimiyya da fasaha na LEADERSHIP Hausa, Husawa ya bayyana cewar matukar ya samu karfafawa daga gwamnati ko wasu kungiyoyi zai iya wadatar da Jihar Bauchi da kayyakin na’urar amfanin yau da gobe. Ga hirar kamar haka:
Ka gabatar mana da kanka don mu san da wa muke tare?
Sunana Adamu Isa Husa wanda aka fi sanina da Adam Husawa, ni haifafen garin Tafawa Balewa ne da ke jihar Bauchi. A can garin na yi rayuwa, daga baya na dawo cikin jihar Bauchi a shekara ta 2002 domin ci gaba da gudanar da ayyukan da na ke yi a halin yanzu. Yanzu haka ina da shekaru kusan 40 a duniya. Na fara gyare-gyare tun ban wuce shekara goma ba, amma kirkire-kirkiren da na fara ne a 2002 kamar yanda na fada maka.
Bincike ya nuna mana Allah ya yi maka baiwa, ka yi mana bayanin irin baiwar da Allah ya yi maka mana?
Daga farko ni dai gaskiya na fara koyon gyare-gyare ne irin su abubuwan da suka shafi mabudin makulli irin su kwadon mota, irin su Raridiyoto da kuma irin abun fitar da rubutu na da (Tafireta) da dai sauransu 1991 zuwa da 2 ne na yi irin wadannan aikace-aikacen. Bayan da na dawo jihar Bauchi a 2002 daga gyare-gyare sai na koma dan kere-kere da kuma kirkire-kirkire na na’urori. Ni idan na zauna na yi nazarin abu na kan zauna na kerashi ne na kuma gwadashi ya yi aiki na gani.
Wasu na fitar na sayar wasu kuma na kan fita da su baje kolin kere-kere a lokuta daban-daban wanda a sakamakon haka na samu nasarori sosai kan abubuwan da na ke gabatarwa a dukkanin wajen da muka je baje kolin kere-kere. Hakan ne ya karfafa min guiwa na ji in kera abu kaza, na sake yin tuni na sake kera wani abun. Na iya samun nasara ne kera abubuwan na’ura da daman gaske a rayuwata.
Wacce irin na’ura ka fara kerawa a rayuwarka?
Abun da na fara kerawa ita ce na’urar bada tsaro (security alarm sabe) wacce take yin ajiya dukkanin abubuwan da mutum ya ga damar ajiyewa domin kiyayeta daga masu mugun hali, idan ka yi saita na’urar ka ajiyeta duk mutumin da ya zo matukar ba shi ne mamallakinta ba, yana tabawa za ta kama kara da ihu. Ita dai wannan na’urar da na fara kyerawa amfaninta ajiya ne, kamar irin su kudi, gwalagwalai ko wasu abubuwa masu muhimmancin da kake son karewa. Sannan kuma tana da gari daga illar wuta da kuma lambobin sirri na koda ka yi nasarar sanya mata ki dinta to sai kuma ka sanya wadannan lambobin sirrin kafin ta budu, matukar baka yi hakan ba to ba za ta bude maka kanta ba.
Da wannan na’urar na fara, daga baya, bayan ganin amfaninta da muhimmancinta sai na sake sabunta ta. Bayan nan kuma sai na zo na fadada kere-kere na zuwa wasu na’urorin kuma irin su Injin kenkesan Kwai, shi wannan na’ura na yi su kala-kala ne, akwai mai amfani da fitilar koyin wutar lantarki akwai kuma mai amfani da abun wuta wanda ba sai na lantarki ba. Bayan wadannan kashi biyun na zo kuma na yi mai kyankyashe kansa da kansa wato (Fafewa) dukkanin wasu abubuwan da sai mutum ya sa hanu ya yi to shi wannan abun zai yi da kansa.
Bayan nan kuma na zo na kirkiri wata na’urar yin fenti, idan ka zuba mata ruwan fenti za ta ke bai wa tsinken yin fentin ruwan da kanta, kai dai na ka kawai shafawa za ka ke yi kana tafiya har ka gama fentinka ba tare da ka doni fenti ko ya shafe ka ba. Sannan kuma tana da wasu amfanoni masu yawa wanda zai zama ya rage maka yawan asarar ruwan fenti, misali idan za ka yi amfani da ruwan fenti lita 20 da hannu, idan da wannan na’urar tawace ba za ka yi amfani da ruwan da ya wuce lita 12 ko 15 ba. Za ta biya maka bukatarka cikin sauki cikin aminci ka samu biyan bukata yanda ya dace.
Bayan wannan, na zo na hada wata inji wacce aikinta busar da kayan abinci, misali za ka iya busar da nama, kifi ko sauran gayyaki ko kuma irin su tumatur duk da wannan injin, shi ma yana amfani ne da wutar lantarki na Nepa ko jannareta. Sannan na zo na kera wasu na’urorin dafa ruwa masu cin lita 20 wanda yanzu haka ana ya yinsu sosai saboda inganci da kuma biyan bukatun da suke yi, domin ya na’urar ya kan iya biya wa manyan gidaje bukatunsu. Ana ya yin wannan hitar sosai.
Na zo na kuma hada wani Inji na shuka, yana nan kamar wilbaro, idan ka sanya masa irinka zai ka ke janshi, shi kuma yana binne maka iri yana kirgawa yana zubawa adadin yanda kake so. Kuma kowace irin noma ana iya sanyawa masa, domin mun yi bakinsa kala-kala ne, daki-daki ana iya cirewa a sanya mai girma ko madaidaici daidai da abun da kake son shukawa, shikafa ne, alkama, ko masa duk dai su na yi.
Sannan kuma mun iya kera firiza mai amfani biyu, a samansa yana sanyaya abu, gidan kasansa kuma maimakon zafin ya ke tafiya a banza sai muka yi masa dabarar da za ka ke iya ajiye abinci ko makamantan abubuwan da kake son ya dumamawa. Sannan kuma, na zo na hada na’ura wacce take taimaka wa kafintoti wajen yanka katakai da dai sauran abubuwa da dama da na ke iya kerawa na kuma fitar domin amfanin mabukata.
Ganin yanda ka ke wandanan kere-keken shin ka yi wani karatun boko ne da ya baka damar samun wannan ilimin ko yaya?
Gaskiya ni karatuna ban wuce sakandari ba, na kwalejin koyon kere-kere da sana’o’i amma gaskiya ni tun farkon shigana da kwarewa ta na shiga, tun a lokacin na shiga ina kan sana’ata ba wai a can an samu ilimi ba. Sai kuma wasu gwaje-gwaje da aka sanya ni na je na yi a wurare daban-daban, mafiya yawan wuraren da ake turani gaskiya ni idan na je suka yi min tambayoyi suka ji abubuwan da na ke yi sai su ga idan na shiga wajen nasu ma ba dai na koyi wani abun ba sai dai ko don na taimaka ta wasu fannonin sai ka ga sun bani satifiket kawai.
Takamaimai a wacce shekara ce ka fara fitar da wata na’ura wacce har ta yi amfani?
Na fara fitar da na’urar security alarm sabe ne a shekara ta 2003 wacce har aka sayeta na zo na sake kera wata, wanda a sanadiyyar ingancinta har ya sani na yi gasar kere-kere wanda na zo na biyu a kan wannan. Wannan cin kofin da na yi shi ne ya bani dama har na fita kasashen waje, da ita wannan abun security.
Kamar yanda na gani, kana hada komai na na’ura sai dai mutum ya dauka kawai ya tafi ya je ya kama aiki da ita. Ya kake yi wajen hadawa?
Yanzu ka gani misali ka je wata kasa ko wani yanki na wannan kasar ka gano wani na’urar da bamu da shi a nan, matukar za ka iya rikewa a kanka yaya ne abun nan ya ke aiki, ka zo ka yi min bayani da baki to zan san abubuwan da zan nema na hada har ya bada abun da ka kawo min, musamman ma idan ni ina da sha’awar abun da ka zo ka min bayani a kansa yanda zan yi ko na kerasa sam baya min wahala. Ni yanzu koda wani aiki ne zan gani, ko wasu da suke wani fanni na aiki matukar ina da sha’awa akan aikin nasu yau da gobe idan ina zuwa to na tabbatar maka zan iya yin wani abu koda ban samu horo kan wannan sana’ar ko aikin ba. Yanzu misali kamar bangarenku na aikin jarida idan ina sha’awar abubuwan da suka shafi labarai ko wani abun da ya shafeku idan da za a kirani a gwadani to idan ma za a yi min gyara zai zama kadan ne. Ni idan ina da sha’awa a kan abu na kan ji ya shigeni kuma idan na lura da yanda ake yin abun to magana ta kare an wuce wajen sai na yi. Matukar na sanya kaina sai na yi nasara a kan abun bana ganin wuyar kirkirar wani abu.
Wasu hanyoyi kake bi wajen samun kayayyakin aikin da kake kere-keren nan naka?
Kayayyakin aiki wasu na kan sayesu ne da kudina, wasu kuma idan na tashi zan yi aikina sai na ga akwai wasu abubuwan da na ke nema amma bana da su ko halinsu, to na kan nemi wajen da suke da irin wannan abun, kamar inda na yi karatu can Bulkeshinal ko jami’ar ATBU ko kuma kwalejin gwamnatin jiha ko na tarayya ko wasu muhallan da suke alaka da teknoloji sai na je na nemi mashin din da ya yi daidai da abun da na ke nema da kuma wanda zai taimaka min wajen gudanar da ayyukan da na sanya a gaba. Ban kuma taba samun matsala na a hanani ko kuma a ki bani dama muhallan da na ambata maka din nan ba.
A wani waje ne kake baje kayan aikinka domin kere-keren?
Wajen da na ke amfani da shi domin aiki, ina cikin Tashan Mass wajen da ake lodin fajinjoji mallakin gwamnati a ciki ne na ke aikina. Daman a cikin waje akwai wasu shagona da aka jima da yi, an kuma tsara su ne domin gyare-gyare da kuma kere-kere sai ya zama an bar wajen haka nan babu wasu kula ba a ma amfani da su domin wajen sun dan yi lungu. Aka kirani aka nuna min wajen aka ce zai yi min na ce zai yi min, sai na amshi wajen na gyara tun daga 2002 har zuwa yanzu a can na ke aikina.
Sau tari wasu ‘yan Nijeriya Allah kan yi musu baiwa na kere-kere za ka tarar wani Allah ya yi masa baiwa na kere abu kaza amma daga baya sai ka ga an dakileshi. Kamar a baya akwai labarin wani wanda ya taba kera jirgi amma daga baya sakamakon da ya zo masa a nan Nijeriya ba mai kyau bane. Kamar yaya kake ji ranka dangane da rashin karfafawa ko ta fuskacin rashin saye ko kuma ita gwamnati ta ki taimakawa?
Gaskiya wannan abun ya jima yana damuna duk wani mai fasahar kera wani abu a Nijeriya za ka kera abu, a zo a gani a yaba. Idan ka nemi taimako sai a gwada za a taimaka maka, ko a sanya ka ka yi ta rubuce-rubuce daga wannan ofis zuwa wancan, daga wannan ma’aikatan zuwa wancan amma daga karshe abun sai ya zo ya zama shiririta.