Zaben fid da gwani na jam’iyyar APC na kokarin fitar da dan takarar gwamna a zaben gwamnan Jihar Edo da zai gudana ranar 21 ga Satumba, ya bar baya da kura, inda a yanzu haka ‘yan takara uku ne ke ikirarin sun yi nasara.
Tun da farko dai, shugaban kwamitin zaben fitar da gwani na APC, Gwamna Hope Uzodinma ya ayyana dan majalisar wakilai, Dennis Idahosa a matsayin wanda ya yi nasara a Otel din Protea da ke Benin, yayin da babban jami’in da ke kula da zaben, Dakta Stanley Ugboaja ya bayyana Sanata Mondaya Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaben a gidan Fasto Osagie Ize-lyamu.
- Blinken: Idan Ba Ka Da Karfi, Za A Cinye Ka
- Gwamnatin Kaduna Ta Tabbatar Da Kashe Jagoran ‘Yan Ta’adda Boderi
Haka zalika, jami’an da suka kula da zaben fitar da gwanin na kanana hukumomi su ayyana Anamero Sundaya Dekeri a matsayin wanda ya yi nasara.
Mai magana da yawun jami’an da suka kula da zaben a kananan hukumomi, Ojo Babatunde, ya sanar da sakamakon zaben ne a daren Asabar, inda ya ce Dekeri wanda ya kasance dan majalisa da ke wakiltar Etsaro a zauren majalisar wakilan Nijeriya, ya samu kuri’u 25,384, wanda ya doke abokin takaransa da ke kusa da shi, Dennis Idahosa da kuri’u 14,127.
Da yake zantawa da manema labarai a Abuja, shugaban kungiyar masu ruwa da tsaki na APC, Emmanuel Godwin ya bayyana cewa Gwamna Uzodinma bai da hurumin daukan nauyin da ya rataya a kan jami’an da suka kula da zaben a kananan hukumomi.
Da yake mayar da martani kan wannan dambarwar, kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC ya dage cewa bisa doka kwamitin da gwamna Uzodinma ke jagoranta shi kadai ne ke da hurumin bayyana sakamakon zaben fitar da gwani na APC Jihar Edo.
Sakataren yada labarai na APC, Felid Morka ya bayyana cewa mutane su yi watsi da duk wani sakamakon da bai cika ka’ida ba.
“Kwamitin gudanarwa na kasa na wannan babbar jam’iyyarmu ya jawo hankalin kan sanar da sakamakon zaben fitar da gwani na APC a Jihar Edo, wanda wasu wadanda ba su da ikon yin haka suke ta yadawa a gidajen talabijin da rediyo da kuma kafafen sada zumunta.
“Muna sanar da cewa kwamitin da Gwamna Hope Uzodinma yake jagoranta ne kadai ke da hurumin bayyana sakamakon zaben fid da gwani na APC a Jihar Edo bisa tsarin doka.
“Muna kira da ‘ya’yan jam’iyyarmu na jihar da kuma sauran mutane cewa su yi watsi da duk wata sanarwa da ba ta cika ka’idar doka ba,” in ji shi.
Idan za a iya tunawa dai, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya kafa kwamitin da zai jagoranta zaben fitar da gwani karkashin shugabancin Gwamna Uzodinma a ranar Alhamis da ta gabata, inda ya ce, “Duk abin da wannan kwamitin ta zantar, to ‘yan takara suna da damar daukaka kara. Domin haka ne ma muke da kwamitin daukaka kara wanda ya kasance kamar kotun koli.”