Gwamnatin Jigawa ta amince da sayan buhunan shinkafa 27,000 da katan na taliya 10,800 domin rabawa jama’a a watan Ramadan.
Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Alhaji Sagir Musa ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Dutse ranar Laraba.
- Tsadar Rayuwa: Yadda Aka Kama Manyan Motoci 4 Na Kayan Abinci A Jigawa
- Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Kashe Naira Biliyan Ɗaya Don Aikin Kiwon Lafiya Kyauta Ga Marasa Ƙarfi A Jihar
Musa ya ce majalisar zartarwa ta jihar ce ta amince da sayan kayaan abincin a yayin zamanta na ranar Litinin.
“Majalisar zartarwar ta Jiha a ranar Litinin, ta amince da wata takarda da ma’aikatar ayyuka ta musamman ta gabatar don bayar da kwangilar sayan hatsi a matsayin tallafin tallafi ga ‘yan jihar a cikin watan Ramadan na 1445AH/2024.
“Majalisar ta amince da sayan buhunan shinkafa 27,000 da kuma katan na taliya 10,800 a matsayin tallafin azumin 1445AH/2024,” in ji Musa.
Ya bayyana cewa an dauki matakin ne domin rage wahalhalun da mutane ke fuskanta sakamakon tsadar kayan abinci a kasuwa.
Kwamishinan ya kara da cewa majalisar ta kuma amince da bullo da wani shiri na musamman da zai bai wa ma’aikatan jihar damar cin gajiyar shirin noma na samar da abinci na Gwamna Umar Namadi.
A cewarsa, shirin mai taken: “Jigawa Worker Agricultural Support Scheme (JWASS), zai bayar da damar samun rancen kayan aikin gona ” ga ma’aikata a kowane mataki.
Musa ya ce makasudin shirin shi ne bai wa ma’aikata damar samun isasshen abinci.