Babban kamfanin rarraba hasken wutar lantarki a Nijeriya (TCN), ya ce, wasu mahara sun lalata layin samar da lantarki mai karfin kilo 330kV na yankin Gwagwalada zuwa Katampe.
Bayanin hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Misis Ndidi Mbah, Babban Manajan Hukumar TCN ta fitar a Abuja ranar Laraba.
“Yawan adadin wutar lantarki da ake samu a Abuja ya ragu da megawatt 250 sakamakon faduwar babbar falwaya ta 70 ta TCN mai karfin 330kV Gwagwalada zuwa Katampe a babban birnin tarayya (FCT).” Cewarta.