Ma’aikatar kula da harkokin kasuwanci ta kasar Sin, ta yi alkawarin tabbatar da gaggauta aiwatar da jerin matakan dake da nufin inganta muhallin zuba jarin waje.
A watan Agustan bara ne majalisar gudanarwar kasar Sin ta fitar da sanarwar da ta zayyana ka’idojin da suka shafi kyautata muhallin zuba jari ga baki, tare da inganta kokarin jawo jari daga waje zuwa kasar.
Yayin wani taron tattaunawa da kamfanoni masu jarin waje, ma’aikatar ta yi alkawarin hada hannu da sassan gwamnati masu ruwa da tsaki da kananan hukumomi, domin nazartar ra’ayoyi da shawarwarin da kamfanonin suka gabatar, da kuma aiwatar da cikakken nazarin ka’idojin, tare da ci gaba da inganta ayyuka ta yadda masu jarin waje za su ci gaba da amfana da manufar. (Fa’iza Mustapha)