Da farko dai abubuwan da ake bukata su ne: Waken Challa, manja, gishiri, bakin ridi, ruwa mai tsafta.
Ana iya yin wannan hanyar dafa abinci tare da wannan wake na musamman wanda aka sani da Waken Challa mai wuyar gaske.
Da farko za ki samu wake ki tsince wake domin kada a samu duwatsu da dattin da ba’a so, sai ki wanke wake ki sa wuta da ruwa mai yawa da gishiri. Dahuwar ya dan dauki lokachi don a tabbatar wake ya dahu sosai har sai ya yi laushi. Bayan waken ya dahu sosai sai ki zuba shi a cikin kwando ya tsane ragowan ruwan jikinsa.
Daga nan ki wanke bakin ridinki sosai sai ki barshi ya bushe a rana, sai ki soya ridinki har ya soyu sosai ki zuba gishiri kadan ki dandana. Ki daka ridinki har ya yi laushi sosai.
Daga ki samu manja ki soya kadan, sai ki zuba a wani kwano ki hada Waken Challa da kika dafa shi da ridinki da kyau sai ki zuba manja dai-dai gwargwado ki juya shi da kyau har ya kai matakin chi, a ci dadi lafiya.