A cikin ’yan shekarun da suka gabata, wasu ’yan siyasa, da kafofin watsa labaru, da masana kimiyya na yammacin duniya, sun shirya jerin labaran karya na cewa “tattalin arzikin kasar Sin na dakushewa bayan da ya kai kololuwa,” da nufin dakile hasashen ci gaban kasar Sin. Musamman tun daga rubu’i na biyu na shekarar 2023, kusan dukkanin manyan kafofin watsa labaru na yammacin duniya, da masana da suka fi maida hankali kan kasar Sin, sun shiga cikin jerin masu sukar tattalin arzikin kasar Sin.
Jaridar Wall Street Journal babban misali ce. Inda daga watan Agustan shekarar 2023 zuwa farkon shekarar 2024, ta wallafa labarai sama da 160, ciki har da mai taken “Karshen bunkasar tattalin arzikin kasar Sin na shekaru 40: Mene ne zai biyo baya?” “Tattalin arzikin kasar Sin ya shiga cikin mummunan da’ira,” da dai sauran su.
- Kakakin Taron Majalisar NPC: Sin Za Ta Ci Gaba Da Kokarin Kare Ikonta Na Mallakar Yankunan Kasa
- An Yi Bikin Tunawa Da Ranar Mata Ta Kasa Da Kasa A Beijing
Sun rufe idanunsu ga hujjoji wadanda ke bayyana bunkasuwar tattalin arzikin Sin a zahiri. Ba wai kawai sun yi kokarin kawo tsaiko ga baiwa alkiblar sauye-sauyen tattalin arzikin kasar Sin damar samun bunkasuwa mai inganci ba, har ma sun yi watsi da gaskiyar cewa kasar Sin ce ke kan gaba a duniya wajen samun bunkasuwar tattalin arziki na hakika.
Misali, kayayyakin da kasar Sin take fitarwa da aka yiwa lakabi da “Sabbin Zakaru Uku” wato kayayyakin sassan makamashin hasken rana wanda a halin yanzu kasar Sin ke rike da kashi 50 cikin dari na kasuwarsa a duniya, da motoci masu amfani da sabbin makamashi wanda a bara ta fitar da guda miliyan 1.2 wato karuwar kashi 77.6 cikin dari, da batirin Lithium inda kamfanonin kasar Sin guda shida ke cikin jerin manyan kamfanoni goma na duniya dake samar da shi. Wadannan sabbin zakaru guda uku suna ba da gagaruwar gudummawa wajen rage tasirin sauyin yanayi tare da bunkasa tattalin arziki kasar Sin. Duk da haka masu sukar tattalin arzikin kasar Sin ba su mai da hankali sun sanya wannan gagarumar ci gabar a cikin labaransu na karyar “dakushewar tattalin arzikin Sin” ba.
Bara mu kwatanta muhimman bayanan tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka a shekarar da ta gabata, farawa da yawan motocin da kasar Sin ta siyar da ya kai miliyan 30.1 wanda ya ninka na Amurka, Yawan danyen karafa da kasar Sin ta samar ya kai sama da tan biliyan 1.02, ya ninka na Amurka sau 12.6, kuma adadin aikin gina jiragen ruwa da kasar Sin ta kammala ya kai nauyin tan miliyan 42.32 wanda ya ninka na Amurka fiye da sau 70. Wadanna nasarori na nuni da karfi da ci gaban tattalin arzikin Sin.
A karshe, yayin da ake zurfafa yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje, tattalin arzikin kasar Sin na kara girma, kuma ana ci gaba da samun bunkasuwa da samun moriyar jama’ar kasar Sin da ma duniya baki daya, tabbas labaransu na karyar cewa “Tattalin arzikin Sin na dakushewa” ba sa tasiri a zukatan jama’a.