Rundunar ‘Yansandan Jihar Adamawa ta sanar da kama shugaban kungiyar Miyetti-Allah na jihar, Alhaji Ja’oji Isa kan zargin aikata zamba.
Wannan na zuwa ne biyo bayan biyan karbar Naira 2.4, a matsayin kudin fansa, da shugaban kungiyar Miyetti Allah a jihar, Alhaji Ja’oji Isa, ya jagoranci karbowa jama’a, lamarin da ya kai ga rundunar sanarwa a kafafen sada zumunta.
- Dubai Ba Ta Dage Haramcin Bai Wa ‘Yan Nijeriya Biza Ba – Fadar Shugaban Kasa
- EFCC Ta Cafke Motoci 21 Makare Da Abincin Da Aka Yi Fasa-kwauri Zuwa Kasashe Makwabta
Rundunar ‘yansandan ta sanar da cewa an gudanar da bincike har ta kai ga kama wanda ya aikata wannan aika-aika.
Sanarwar ta ce kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Dankombo Morris, na da kudirin tabbatar da mafi girman matakan gaskiya da rikon amana.
Ya kuma bayar da umarnin a gudanar da bincike domin tabbatar da cewa wannan mugunyar dabi’a ta garkuwa da mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, ba ta ci gaba ba.
Ya kuma jaddada cewa ya zama wajibi wadanda aka samu da laifin cin amanar jama’a su fuskanci hukunci.
Wannan na kunshe cikin sanarwar manema labarai da kakakin rundunar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya sanya wa hannu.
“A matsayinmu na masu kare lafiyar jama’a, dukiyoyi da tabbatar da bin doka da oda, mun jajirce matuka wajen tabbatar da ganin an ci gaba da rike amanar jama’a kuma za mu ci gaba da daukar kwakwaran mataki kan duk wani mai laifi,” in ji sanarwar.