Da safiyar yau Alhamis, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya kira wani taron manema labarai a gefen taro na 2 na Majalisar Wakilan Jama’ar Kasar Sin karo na 14, inda ya amsa tambayoyin ’yan jarida game da manufofin Sin da dangantakarta da kasashen waje.
Da aka tabo dangantakar Sin da Afrika, Wang Yi ya ce Sin da Afrika sun kasance ’yan uwan juna masu makoma ta bai daya. Kuma a matsayin babbar abokiyar huldar cinikayya ta nahiyar Afrika tsawon shekaru 15 a jere, nasarorin da huldar bangarorin biyu ta samu na kara habaka, lamarin dake kara kusancin zukatan al’ummominsu.
- Sabuwar Cuta Ta Hallaka Mutane 30 A Gombe
- Li Qiang: Kamata Ya Yi Yunnan Ya Yi Amfani Da Fifikonsa Don Shiga Cikin Tsarin Rayawa Da Daidaita Harkoki Baki Daya Tsakanin Yankuna
Yanzu haka, dangantakar kasashe masu tawo da Sin da Afrika ke wakilta, tana yin gagarumin tasiri ga tarihin duniya. Ya ce kasashen Afrika sun shiga wani sabon yanayi, inda suka gane cewa tsare-tsaren da aka kakaba musu daga waje, ba su haifar musu da kwanciyar hankali ko wadata ba. Ya ce akwai bukatar nahiyar Afrika ta lalubo hanyar da ta dace da yanayin kasashenta da kuma tsara makomarta da take so da kanta. A cewarsa a wannan sabon yanayin na tarihi, kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa da ’yan uwanta kasashen Afrika da mara wa nahiyar baya wajen tabbatar da ainihin ’yancinta, da taimaka mata inganta samun ci gaba bisa dogaro da kanta da kuma gaggauta tsarin zamanantar da nahiyar.
Wang Yi ya kara da cewa, a ko da yaushe, kasar Sin ta kasance mai adawa da nuna wariya ga nahiyar Afrika. Ya ce bayan irin dimbin ci gaba da dangantakar Sin da Afrika ta samu, yanzu wasu manyan kasashen duniya suna mayar da hankalinsu kan nahiyar Afrika, kuma Sin na maraba da hakan. Ya ce yana fatan dukkan bangarori, kamar Sin za su kara mayar da hankali kan nahiyar, da kara zuba mata jari da taimakawa ci gabanta. Haka kuma, suna maraba da shiga hadin gwiwa da karin kasashe bisa sharadin girmama dukkan bangarori.
A lokacin kaka na bana, za a gudanar da wani sabon taron koli na dandalin tattauna dangantakar Sin da Afrika a kasar Sin, inda shugabannin Sin da Afrika za su kara haduwa a Beijing bayan shekaru 6, domin tattauna makoma da tsare-tsaren ci gaban da na raya dangantakarsu da zurfafa musaya kan dabarun shugabanci. Game da hakan, ya ce ya yi imanin cewa, ta hanyar wannan taro, Sin da Afrika za su kara yaukaka dangantakarsu ta abota da zurfafa hadin kai da dangantaka da bude sabon babi na samun al’ummar nahiyar Afrika da Sin mai makoma ta bai daya. (Mai Fassarawa: Fa’iza Msutapha)