Babban jami’i a ofishin wakilcin Sin na MDD Dai Bing, ya yi kira ga kasashen duniya da su tallafawa matakan siyasa a kasar Sudan. Dai Bing ya ce dorewar rikicin Sudan, ya haifar da asarar rayukan fararen hula masu tarin yawa, da mummunan yanayin jin kai, don haka ya dace sassan kasa da kasa su yi aiki tare wajen zakulo dabarun warware rikicin kasar ta hanyar siyasa, da gaggauta dawowa da zaman lafiya.
Jami’in ya kara da cewa, Sin na goyon bayan hadin gwiwar kungiyar tarayyar Afirka ta AU, da ta raya gabashin Afirka IGAD, da sauran kasashe makwabtan Sudan, wajen shiga tsakani a rikicin na Sudan.
Kaza lika, Dai Bing ya ce kamata ya yi kasashen duniya su tallafi kokarin da shiyyoyi ke yi a wannan fanni, su martaba ikon mulkin kai na Sudan, da ikon kare yankunan ta, kana su kaucewa tilastawa kasar daukar matakan ketare na warware matsalolin da take fuskanta. (Saminu Alhassan)