Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yau Jumma’a 8 ga wata cewa, kwanan nan ne, kasar Amurka na yawan cin zarafi, bincike, da kuma dawo da daliban kasar Sin dake kasar saboda dalilai na siyasa, kuma Sin ba ta gamsu da hakan ba, har ma tana adawa da hakan, kana ta riga ta nuna matukar takaici ga bangaren Amurka.
A yayin taron manema labaru da aka saba yi a yau, jami’ar ta ce, kasarta ta bukaci Amurka da ta daina muzgunawa daliban kasar Sin da ke karatu a kasar Amurka, bisa hujjar “tsaron kasa”, da daina kawo illa ga muhallin ra’ayin jama’a na dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da dakatar da kawo cikas ga mu’amalar sada zumunta tsakanin al’ummomin kasashen biyu. Kasar Sin za ta dauki kwararan matakai don kiyaye halaltattun hakkoki da muradun ‘yan kasar. (Mai fassara: Bilkisu Xin)