Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ƙaddamar da wani sabon rukuni na biyan kuɗaɗen sallama ga tsofin ma’aikatan jihar da na ƙananan hukumomi su fiye da mutum 4,000 da suka yi ritaya daga aiki tare da yin alkawarin biyan sauran haƙƙoƙin ma’aikatan da suka yi ritayan.
A wannan karon, gwamnatin jihar za ta biya kuɗaɗen sallaman da suka kai Naira biliyan 5 da miliyan 440 da dubu 45 da 865 da Kobo 73 ga tsofin ma’aikatan na jiha da ƙananan hukumomi.
- Ramadan: Maryam Abacha Ta Nemi Attajirai Su Tallafa Wa Mabukata
- An Kammala Canja Fasalin Gasar Cin Kofin Zakarun Turai
Hakan dai yana nufin an rage basussukan da tsofin ma’aikatan ke bin gwamnati daga naira biliyan 21 zuwa Naira biliyan 7, kamar yadda Ismaila Uba Misilli ya tabbatar a sanarwar da ya aiko mana.
Da ya ke jawabi yayin bikin da aka gudanar a gidan gwamnati, Gwamna Inuwa Yahaya ya jaddada ƙudurin gwamnatinsa na inganta jin dadin ma’aikata dama waɗanda suka yi ritaya, yana mai yaba wa irin gudunmawar da suke bayarwa ga ci gaban Jihar Gombe.
Gwamnan ya tuno cewa bayan hawansa mulki a 2019, ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da gwamnatinsa ta gada shi ne na bashin fiye da naira biliyan 21 na kuɗaɗen giratuti da waɗanda suka yi ritaya suke bin gwamnatin jihar da ƙananan hukumomi.
Ya ci gaba da cewa, a ƙoƙarinta na tabbatar da gaskiya da adalci, gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancinsa ta ba da fifiko wajen magance matsalar baki ɗaya, don haka cikin shekaru biyar da suka gabata ta biya fiye da Naira biliyan 7 na bashin kuɗaɗen giratutin da ta gada.
Ya ce, “A wannan zagayen, za mu biya kuɗaɗen da suka kai naira biliyan 5 da miliyan 440 da dubu 45 da 865 da Kobo 73 ga wasuka yi ritaya daga jiha da ƙananan hukumomi. Gwamnatin jihar za ta biya giratuti na shekarar 2018, ƙananan hukumomi kuma za su biya ne gwargwadon ƙarfin aljihun kowace ƙaramar hukuma, inda ƙananan hukumomi masu karfin tattalin arziƙi za su iya biyan fiye dana takwarorinsu masu ƙaramin ƙarfi,” in ji Gwamnan.
Ya ƙara da cewa, “Don haka ƙananan hukumomin Kwami, da Funakaye da Nafaɗa za su iya biyan duk bashin giratutin da ake binsu; Akko da Ɓillliri, da Dukku da Shongom za su biya giratuti na 2014 da 2015, Balanga da Yamaltu Deba kuma za su biya na 2013 da 2014, yayin da Kaltungo da Gombe za su biya waɗanda suka yi ritaya na 2013 ne kawai. Wannan tsarin zai taimaka sosai wajen ƙarfafa gaskiya da riƙon amana, don ya dace da kowace ƙaramar hukuma.
Gwamna Inuwa Yahaya ya yi ƙira ga ma’aikatan jihar su ruɓanya ƙoƙari tare da nuna jajircewarsu wajen gudanar da ayyuka, inda ya bayyana kwazo da jajircewarsu masu a matsayin ɗaya daga cikin nasarorin gwamnati mai ci.
Gwamnan ya yi gargaɗin cewa “Gwamnatinmu ba za ta lamunci duk wani nau’i na rashin ɗa’a ko rashin gaskiya da zai iya ɓata sunan ma’aikatan gwamnati dama na Jihar Gombe baki ɗaya ba, muna sa ran kowane ma’aikacin gwamnati ya nuna kyakkyawan misali na gaskiya, ƙwarewa da kuma riƙon amana a halaye da mu’amalarsa”.
Gwamnan ya yabawa shugabannin kwadago, da shugabannin ƙungiyoyin ma’aikatan da suka yi ritaya, da sauran masu ruwa da tsaki bisa haƙuri, fahimta, haɗin kai da kuma jajircewarsu wajen tattaunawa a lokacin da ake kokarin magance koma-baya da aiwatar da gyare-gyare a harkar aikin gwamnati.
Tun farko a jawabinsa na maraba, babban mai binciken kuɗi na jiha kuma shugaban kwamitin biyan giratutin Muhammad Buba Gombe, ya amince da ƙoƙarin da gwamnan ya yi wajen magance matsalar rashin biyan giratuti tun hawansa mulki a 2019.
Ya ƙara da cewa sakamakon wannan amincewar na baya-bayan nan, jimillar kuɗaɗen gratutin da gwamnatin ta biya sun kai Naira biliyan 12, miliyan 736 da dubu 228 da 885. Ya zuwa yanzu mai girma gwamna ya amince da biyan kudin giratuti na tsofin ma’aikatan jiha dana ƙananan hukumomi”.
Da yake jawabi a madadin ɗokacin waɗanda za su ci gajiya, Garba Sama’ila, ya godewa Gwamna Inuwa da ya kawo musu ɗauki a wannan mawuyacin lokaci na taɓarɓarewar tattalin arziƙi.
Yace da wannan karimcin, Gwamnan ba kawai biyan giratuti ga ma’aikatan da suka yi ritaya ya yi ba, har ma da ceto ga miliyoyin iyalansu daga mummunar matsalar tattalin arzikin da ake ciki a yau.
Malam Garba ya kuma yi alkawarin cewa duk waɗanda suka yi ritayan za su mara baya ga tsare-tsare da manufofin gwamnatin Inuwa, inda ya bayyana Gwamnan a matsayin “shugaba mai jin ƙai kuma aminin waɗanda suka yi ritaya”.
Muhimman ababen da suka fi ɗaukar hankali a taron su ne gabatar da cekin kuɗi ga waɗanda suka yi ritayar, waɗanda galibinsu suka bar aikin tun a shekarar 2013 amma ba su sami hakkokinsu ba.