Akwai ababen da suke ci mun tuwo a kwarya cikin mu’amalat na rayuwar yau da kullum da suke gudana a gaban idona….
Cewar daya daga cikin marubutan littattafan hausa na yanar gizo kenan wato FARIDAT HUSSAIN MSHELIA wacce aka fi sani da *UMMU JIDDA* inda take bayyanawa masu karatu dalilan da suka ja hankalinta har ta tsunduma harkar rubutu. Ga dai tattaunawar tare da PRINCESS FATIMA ZARAH MAZADU Kamar haka:
Ya sunan Marubuciyar?
Sunana Faridat Husain Mshelia wacce aka fi sa ni da Ummu Jidda.
Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
An haife ni a karamar hukumar Suleja Jihar Neja ce an haife ni 1995, Mahaifina dan kasar Borno ne, Babur ce ni a takaice, bangaren uwa kuwa Hausa/Fulani nake. Na yi karatun boko dana addini duka a garin Suleja, ni matar aure ce ina da miji da ‘ya’ya 4.
Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma harkar rubutu?
Son wayar da kan mata da fadakar da su don akwai ababen da su ke ci mini tuwo a kwarya a cikin mu’amalat na rayuwar yau da kullum da su ke guduna a gaban idona, sai na lura rubutu hanya ce mafi sauki na isar da sako ga miliyoyin mutane, wannan dalilin ya sa na afka harkar rubuce-rubuce babu kama hannun yaro.
Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?
Gwagwarmaya ta fara tun lokacin da na rasa bango majinginata (Mahaifina) a shekarar 2011, kadaici da damuwa ya sa nake kebewa a daka da takarda da biro ina rubutu duk da ada karatu ne abincin ruhina, kwatsam bayan rasa jigona na fara rubutu kamar wasa, idan na rubuta sai in tara kannena da mahaifiyata in karanta musu sai su yi ta yaba mini da ya yi dadi. Wannan karfafar gwiywar ta so shi ya fara busa mini ruhin tabbas zan iya don haka ko da na yi aure a shekarar 2012 na ci gaba da rubuce-rubuce har na rubuta littafi guda 2 sai dai a wannan lokacin ba ni da halin buga su, kwatsam sai na tsinci kaina a manhajar Facebook, dandalin da wasu tsirarrun Marubuta ke baje kolin fasaharsu, na bi yarima na sha kida don a matsayin makaranciya na afka ina karantar yanayin ni ma na fara rubuta wani littafi mai suna “Auren Dole” babu laifi ya karbu duk da ba shi ne littafin da ya sanya na yi shura ba a lokacin.
Kin rubuta labarai sun kai kamar guda nawa?
Sun kai kamar guda 10; Sanadin Facebook, Auren Jari, Mutuncinki ‘Yancinki, Ita ce sila, First Ramadan with Habibi, Sun Guje Ni, Yawon Ta Zubar, Bestyn Mijina, Soyayya Lokacin Kulle, Sai wanda na ke kan rubutawa AN ƘI CIN BIRI…
Kin taba buga littafi?
Ban taba buga labari ba sai dai da na shiga gasar ‘Aminiya daily trust 2020’, an buga mana littafi wanda ya kasance na hadaka mai suna Sakamakon gasar Aminiya, labarina yana ciki, ina da burin buga labarin AN ƘI CIN BIRI…. in sha Allahu.
Wane labari ne cikin labaran da ki ka rubuta ya zamo bakandamiyarki?
Kowanne bakandamiyata ce.
Wane labari ne ya fi baki wuya wajen rubutawa?
Littafin SUN GUJE NI ya fi bani wahala saboda labari ne da ya shafi wata cuta don haka yana bukarar bincike, kasancewar shi ‘true life story’ ne ya sa ya kara bani wahala sosai.
Wane irin kalubale ki ka fuskanta game da rubutu?
Cikin karfin gwiwa na fara rubutu, sai dai dan kalubalen da duk wanda ya fara abu ba zai yu ace ya rasa ba, kamar na rashin sabawa da mutane da sauran matsalolin da ke baibaye da dukkannin mai koyon abu amma duk da tarin kalubale nasarorin sun fi yawa. A gida kuwa ban samu kalubale ba sai karfafa mini gwiwa da Mahaifiyata ta yi, duk da lamarin kamar da wasa-wasa amma koda yayana ya san ina yi sosai ya karfafa mini gwiwa da shawarwari hade da koyar da ni dabaru masu yawan gaske.
Wane irin nasarori ki ka samu game da rubutu?
Haduwa da mutanen kirki daga Marubuta da Makaranta shi ne babban nasarar da na samu na farko a harkar rubutu, in da wasu sun zamto mini kamar ‘yan’uwa na jini, wasu matsayin kawaye, wasu matsayin iyaye, idan na ce iyaye ina nufin na samu uwar da ta mayar da ni diyar cikinta duk a sanadin rubutu kin ga wannan nasarar yana sanya ni jindadi matuka gaya. Nasara ta biyu shiga gasanni da daruruwan Marubuta ke shiga a fafata wani na yi nasara wani kuma na fadi duk da a gurina shiga gasar a karan kan shi nasara ne cikin wanda na shiga na yi nasara shi ne na gasar Aminiya daily trust 2020, in da labarina ya shiga jerin 15 wanda suka cancanci yabo, sai gasar da BBC HAUSA ke sanyawa a duk shekara na Hikayata in da shi ma na fito cikin mutane 12 da labarinsu ya cancanci yabo har na samu tagomashin samun satifiket in da na zo ta 5, wannan nasara ce wanda ban taba tunanin zai kai gare ta ba tabbas yin Allah ne ba yi na ba ne don akwai gwanayen da suka fini iyawa da yawan gaske amma ya zabe ni daga cikinsu don haka nake gGodiya a gare shi da wannan nasarar.
Kamar wanne bangare ki ka fi mayar da hankali a kai wajen yin rubutu?
Labarin da na fi mayar da hankali wajen rubutawa shi ne matsalolin da su ke ci mini tuwo a kwarya misali; labarin da ya danganci Mata masu kazanta, yadda matan aure da mada ke sangarcewa a yanar gido (Media), labaran soyayya da sauransu a takaice na fi mayar da hankali wajen yin rubutu akan zamantakewa da addini da al’ada.
Mene ne burinki na gaba game da rubutu?
In taka matakin da zan jagoranci Marubuta masu tasowa don ciyar da adabi gaba.
Me ya fi faranta miki rai game da rubutu?
Yadda na tsafta ce alkalamina na ke rubutun da ke kawo gyara ga rayuwar ‘yan’uwana mata da al’umma gaba daya idan na tuna sakon na kai wa gurin da ya kamata ya je hakan na faranta mini rai.
Bayan rubutu kina wata sana’ar ne?
Ina sana’ar da ya shafi cikin gida sannan a social media ina taba harkan cryptocurrency.
Ya ki ke iya hada sana’arki da kuma rubutu?
Kowanne ina ba shi lokacin shi na musamman don haka bani da wani matsala kuma sana’ar da nake yi ba mai takura ba ne.
Kamar da wane lokaci ki ka fi jin dadin yin rubutu?
lokacin da sawaye suka ɗauke, kukan tsuntsaye suka kawata na zumayena a takaicen dai ina nufin idan dare ya tsala ko asuba ko kuma idan guri ya yi shiru ba hayaniya ina jin dadin yin rubutu a wannan lokacin koda da rana ne.
Me za ki ce da makaranta labaranki?
Alhairin Allah da alhairin shi ya tabbata gare ku, ina alfahari da ku a rayuwa ku ne ni, ni ce ku don da bazar ku nake taka rawa don haka ina yi muku fatan alhairi da gamawa da duniya lafiya.
Ko kinada wadanda za ki gaisar?
Uwa ba da Mama (Mahaifiyata)
Momina Malama Ruƙayya (Principal), Hadiza D Auta (Kakus),
Maman Nusy (Sarat alƙasim), Antina Aisha Mshelia.
Ki huta lafiya.
Na gode.