Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon ta’aziyya ga shugabar kasar Tanzania Samia Suluhu Hassan a ranar 7 ga wannan wata, dangane da rasuwar tsohon shugaban kasar Ali Hassan Mwinyi. Kana a madadin gwamnati da jama’ar kasar Sin, ya jajantawa gwamnatin kasar Tanzania da jama’arta da iyalan tsohon shugaba Mwinyi.
Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, tsohon shugaban kasar Tanzania Ali Hassan Mwinyi, dan siyasa ne kuma shugaba na kwarai, kana abokin jama’ar kasar Sin, wanda ya bayar da muhimmiyar gudummawa ga raya dangantakar dake tsakanin Tanzania da Sin. Ya kara da cewa, kasar Sin tana dora muhimmanci sosai kan sada zumunta tsakaninta da kasar Tanzania, haka kuma tana son hada hannu da kasar Tanzania wajen fadada hadin gwiwa da sada zumunta a dukkan fannoni, da sa kaimi ga inganta dangantakar abota ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp