• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

In Sa Ya Rika Dole Ya Yi Tozo: Kwarewar Kasar Sin Na Kara Zaburar Da Duniya

by CGTN Hausa
2 years ago
Sin

“Taruka Biyu” wato taron majalisar ba da shawara kan hankokin siyasa CPPCC da na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC da aka kammala a jiya Lahadi 10 da yau Litinin 11 ga wata, harkar ce ta cikin gidan kasar Sin, amma tasirin kasar Sin a duniya da barbashin bunkasar tattalin arzikinta da salonta na zamanintar da kasa da al’ummarta na shafar duniya baki daya musamman kasashe masu tasowa wanda ya zama abin nazari ga sauran kasashen duniya.

A yayin tarukan biyu, manazarta da masu sa ido a duniya sun yi bibiyar sanarwa game da manufofi da shawarwarin tattalin arziki don kara fahimtar hanyar da kasar Sin ke bi wajen bunkasa tattalin arziki da zamanintar da jama’a. Sun ce kwarewar kasar Sin na kara zaburar da duniya, musamman kasashe masu tasowa.

  • An Wallafa Littafi Na 1 Da Na 2 Na Littafin “Zababbun Kalamai Daga Jawaban Xi Jinping” Cikin Harshen Ingilishi
  • CPPCC Ya Rufe Cikakken Taronsa Na Shekara-shekara 

Nasarar kyautata zamantakewar kasar Sin na nufin zamanantar da dimbin jama’a, da wadata ga kowa da kowa, da raya kayayyakin tarihi da al’adu, da daidaito tsakanin bil’adama da yanayi, da samun ci gaba cikin lumana.

Hanyar da kasar Sin ta bi game da zamanantarwa ta samo asali ne daga “wayewar da take da ita.” La’akari da bambance-bambance tsakanin salon zamanantarwa ta kasar Sin da kuma hanyar da kasashen yammacin duniya ke bi wajen neman zamanantarwa, ya sanya Cavince Adhere, wani masani kan huldar kasa da kasa dake zaune a kasar Kenya, tabbatar da cewa “hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin ta zama abin sha’awa ga kasashe masu tasowa,” wadda ta ginu a kan turbar zaman lafiya, da kyakkyawar niyya ga sauran kasashe, da kuma mai da hankali kan kyautata rayuwar bil’adama baki daya, wanda ya bayyana dalilin da ya sa kasar Sin ke more fasahohin neman ci gabanta ga sauran kasashen duniya.

A zahiri muna iya ganin musabbabin nasarar kasar Sin ta yadda take inganta zaman lafiya da ci gaba tare da darajta girman kasuwarta, da tsarin ilimi mai zurfi, da hada-hadar kasuwanci da siyasa, da kuma babbar kasuwar hada-hadar kudi, da kyautata yankunan cinikayya maras shinge tare da mai da hankali kan tallafawa tsarin fitar da kayayyaki daga kasuwar gida zuwa kasashen waje a matsayin muhimman abubuwan da ke cikin salon zamanantarwata.

LABARAI MASU NASABA

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

Keith Bennett, wani mai ba da shawara kan huldar kasa da kasa dake Landan ya bayyana cewa, “Duk da cewa zamanantarwa tsari ne na duniya da kuma buri na duniya, za ta iya daukar salo da kuma nau’i daban-daban.” Amma zamanantarwa irin ta kasar Sin “tana wakiltar wani sabon abu ne” wato wani abu da za a iya ganinsa a matsayin zamanantarwa ta hakika kuma a zahirance, cikakke, mai daidaito da kuma dorewa.

Masana da masu bibiyar yanayin ci gaban duniya sun shaida yadda kasar Sin ke kokarin samar da damar zamanantar da duniya, ta hanyar raba kwarewarta da kasashe masu tasowa da ba da gudummawar fasahohi da albarkatun kudi da na kwadago, kuma tana hakan ne saboda ai “idan Sa ya rika dole ya yi tozo”.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo
Daga Birnin Sin

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

November 7, 2025
Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta
Daga Birnin Sin

Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

November 7, 2025
Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

November 7, 2025
Next Post
Wakiliyar CPPCC Wadda Take Kokarin Neman Mafita Ga Sha’anin Kiwon Reindeer

Wakiliyar CPPCC Wadda Take Kokarin Neman Mafita Ga Sha’anin Kiwon Reindeer

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri 4, Sun Ƙwato Makamai A Filato

Zaben Kananan Hukumomi A Neja Ya Bar Baya Da Kura

November 7, 2025
Gwamnatin Zamfara Ta Ɗauki Malaman Makaranta 500 Aiki

Gwamnatin Zamfara Ta Ɗauki Malaman Makaranta 500 Aiki

November 7, 2025
GORON JUMA’A

GORON JUMA’A

November 7, 2025
Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja

Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja

November 7, 2025
Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)

Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)

November 7, 2025
Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

November 7, 2025
Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima

Hanyoyin Noma Na Gargajiya Ba Za Su Iya Wadata Abinci A Nijeriya Ba -Masanin Kimiyya

November 7, 2025
An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

November 7, 2025
Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

November 7, 2025
Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.