Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da kashe Naira biliyan 2.8 domin ciyar da mabukata da marasa karfi a jihar a watan Ramadan.
Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis a Dutse.
- Ramadan: Gwamnatin Jigawa Za Ta Ciyar Da Mutum 171,900 A Kullum Da Azumi – Namadi
- Hisbah A Kano ta Cafke Mutane 11 Bisa Laifin Cin Abinci A Lokutan Azumin Ramadan.
Musa ya ce, an dauki matakin ne a taron majalisar zartarwa na jihar da ya gudana a ranar Laraba, 13 ga watan Maris.
Ya ce, an amince da shirin ne domin tallafawa al’umma sakamakon hauhawar farashin kayayyakin abinci da ake fuskanta a kasar.
Kwamishinan ya kara da cewa, majalisar ta kuma amince da cibiyoyin ciyar da abinci guda 609 a fadin jihar domin ciyar da abincin a watan Ramadan, inda ya ce, akwai a kalla cibiyoyi biyu a kowacce unguwa 287 da ake da su a fadin jihar.