Daga ranar 18 zuwa 20 ga wata, an kira “taron koli na demokuradiyya” karo na uku a kasar Koriya ta kudu, wanda Amurka ta ba da shawarar gudanar da shi. Amma al’ummar duniya na kara kin amincewa da demokuradiyya irin ta kasar Amurka, har wasu suna kallon Amurka a matsayin barazana ga kokarin da ake yi na wanzar da demokuradiyya a duniya.
Dalilai biyu ke haifar da rashin amincewa ga demokuradiyya irin ta Amurka, wato munafunci da girman kan da Amurka ke da su a wannan bangare.
- Sin Ta Harba Tauraron Dan Adam Na Queqiao-2
- CMG Ya Shirya Taron Tattaunawa Tsakanin Kafofin Watsa Labaran Kasa Da Kasa A Najeriya
A ‘yan shekarun baya, ‘yan siyasar Amurka sun sha fakewa da sunan demokuradiyya a yunkurin kiyaye babakerensu a duniya, inda suka yi amfani da demokuradiyya a matsayin wani makami don shafawa wasu bakin fenti. A hakika dai, cibiyar nazarin harkokin demokuradiyya da zabe ta duniya, tuni ta ajiye Amurka a matsayin kasa mai koma baya a fannin demokuradiyya.
Ban da haka, Amurka ita ce ta zabi kasashen da take ganin sun cancanta wajen halartar taron, ta kuma raba kasashen duniya zuwa kashi biyu, don tada sabani tsakaninsu. Matakin da ya saba wa ka’idar demokuradiyya kuma ya keta akidunta.
Irin wannan taro maras sahihanci da gaskiya, ba ya da alaka da demokuradiyya balle ma a ce ya kawo tasiri mai yakini ga kokarin da ake yi wajen wanzar da demokuradiyya a duniya. Kamar yadda jaridar “The Standard” mai tsawon tarihi ta kasar Kenya ta bayyana a cikin sharhinta, “da ma ana sa ran taron kolin demokuradiyya ya zama wata fitila wajen samar da makoma mai haske, amma abin bakin ciki shi ne, taruka biyu da aka yi a baya da ma taron da ake yi a wannan karo, dukkansu sun shaida cewa, ba su da alaka ko kadan da demokuradiyya, girman kai ne kawai taron ke nunawa”. (Mai zane da rubutu: MINA)