Hedikwatar tsaron Nijeriya, ta bayyana cewa dakarunta da hadin guiwar sauran hukumomin tsaro sun ceto ‘yan makaranta 137 da aka sace a Kuriga da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.
Daraktan yada labarai na rundunar, Manjo Janar Edward Buba, ya ce yaran da aka ceto sun hada da mata 76 da maza 61 da safiyar Lahadi 24 ga Maris, 2024, a wani wuri a jihar Zamfara.
- An Sako Ɗaliban Makarantar Kuriga Da Aka Sace A Kaduna – Uba Sani
- Mahara Sun Sace Dalibai 200 A Kauyen Kaduna
Idan ba a manta ba LEADERSHIP HAUSA a ranar 7 ga Maris, 2024 ta rawaito muku yadda wasu ‘yan ta’adda suka kai hari makarantar LEA Kuriga, karamar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da ‘yan makaranta 287.
Gwamnatin tarayya dai ta umurci sojoji da su tabbatar an dawo da yaran makaranta lafiya.
A baya LEADERSHIP ta kawo rahoto kan cewa an kubutar da daliban, a cewar gwamnan jihar Uba Sani, wanda ya sanar da farko game da ceto yaran ba tare da bayyana adadin wadanda abin ya shafa ba a safiyar yau Lahadi.
Sai dai a cewar sanarwar ta hedikwatar tsaron Nijeriya ta cfurta ya saba da alkaluman farko na adadin daliban da sojojin suka ce sun yi nasarar kubutar da su.
“A ranar Lahadi, 24 ga Maris, 2024, sojojin da ke aiki tare daw hadin guiwar wasu hukumomi sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.
“Wadanda aka yi garkuwa da su daga makarantar da ke Kuriga a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.
“Dalibai 137 da aka yi garkuwa da su sun hada da mata 76 da maza 61, an ceto su ne a jihar Zamfara kuma za a mika su ga gwamnatin jihar Kaduna,” inji Manjo Janar Buba.
Rundunar sojin ta ce za a ci gaba da kokarin har sai an gano ragowar mutanen da aka yi garkuwa da su da tabbatar da an kama ’yan ta’addar an yi musu an gurfanar da su gaban shari’a.