Gwamnatin tarayya ta ce, ta gayyaci fitaccen malamin addinin musuluncin nan na Kaduna, Ahmad Gumi domin amsa tambayoyi kan kalaman da ya yi kan ayyukan ‘yan bindiga a kasar nan.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin da yake jawabi ga manema labarai a fadar gwamnati, da ke Abuja.
- Tauraron Dan Adam Na Queqiao-2 Ya Shiga Falakinsa A Zagayen Wata
- Gwamnatin Nijeriya Ta Yaba Da Ƙwazon Tawagar ‘Yan Nijeriya A Wasannin Afirka
Idris ya ce, Gumi bai fi karfin doka ba, don haka gwamnati ta ga ya dace ta gayyace shi domin amsa tambayoyi.
A cikin ‘yan shekarun da suka gabata, Sheikh Gumi ya yi fice wajen yin tsokaci kan ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a kasar nan.