Shugaban kasa, Bola Tinubu a yayin da yake farin ciki da labarin sakin daliban makarantar Kuriga da ke jihar Kaduna, ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi domin samun sakamako mai kyau, musamman kan harkokin tsaro.
Wannan dai na zuwa ne yayin da tawagar Sufeto Janar na ‘yansanda na musamman 200 suka isa jihar Kaduna ranar Lahadi.
- Dalibai 137 Aka Sace A Kuriga Ba 287 Ba – Uba Sani
- Ɗaliban Kuriga 137 Muka Yi Nasarar Kuɓutarwa A Zamfara, Ba Ɗalibai 287 Ba— Sojoji
Shugaban, a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata, ya yabawa mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, da hukumomin tsaro, da kuma gwamnatin jihar Kaduna bisa wannan namijin kokari da jajircewa da suka yi wajen kubutar da ‘yan makarantar.
Tun a ranar Lahadin, gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa an sako yaran makarantar Kuriga 137 da aka sace ba tare da sun samu wani rauni ba.